An cafke kasurguman 'Yan fashi da Makami da Garkuwa da Mutane a jihar Benuwe

An cafke kasurguman 'Yan fashi da Makami da Garkuwa da Mutane a jihar Benuwe

Tsaro mai tsanani tare da tsayuwar daka kan magance miyagun ta'addanci tsawon makonni hudu da suka gabata a jihar Benuwe ya tsananta, tun yayin da sabon kwamshinan 'yan sanda na jihar, Mista Ene Okon ya karbi ragamar jagoranci.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya bayyana, Mista Okon tun yayin karbar ragamar jagorancin tsaro a jihar ya kawar da shakku da tantama kan akidarsa ta tsarkake duk wasu lunguna da sako na jihar daga miyagun ta'addanci masu tayar da zaune tsaye.

A sanadiyar wannan kwazo da kwarewar aiki ya sanya cikin kankanin lokaci kwamishin ya cafke wani matashin dan ta'addan mai shekaru 25 kacal a duniya, Aondowase Emberga, da ya shahara da sanya kakin sojin wajen addabar al'ummar jihar da kewaye.

Emberga ya shiga hannu tare da wasu mambobi 5 na kungiyar sa da suka shahara kan ta'addanci na fashi makami musamman ga Matafiya masu bibiyar babbar hanyar birnin Makurdi zuwa birnin Lafia na jihar Nasarawa.

An cafke kasurguman 'Yan fashi da Makami da Garkuwa da Mutane a jihar Benuwe
An cafke kasurguman 'Yan fashi da Makami da Garkuwa da Mutane a jihar Benuwe
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa, Emberga ya shiga hannu yayin da jami'an tsaro ke kwakwule gami da bincike irin na sakace a wani daji da sai kacibus suka yi da wannan dan ta'adda sanye cikin kakin soji da raunuka na harsashin bindiga a kafar sa.

KARANTA KUMA: Bayyanar Hotunan wasu Maza biyu da suka auri junan su ya janyo cecekuce a Zaurukan sada zumunta

Wannan bincike ya biyo bayan aukuwar wani artabu na musayar wuta tsakanin jami'an 'yan sandan da kuma 'yan ta'adda a yayin da suka fito cin kasuwar su ta fashi da makami.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata babbar kotu ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani karamin jami'in dan sanda da aka kama shi dumu-dumu da laifin kisan gilla ba tare da hakki ba a jihar Bayelsa.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel