Da dumi dumi: Gwamnonin PDP sun rantse ba zasu goyi bayan kowanne dan takara ba

Da dumi dumi: Gwamnonin PDP sun rantse ba zasu goyi bayan kowanne dan takara ba

- Gwamnonin PDP sun ki amincewa da marawa dan takara daya 'tilo' a zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa

- Gwamnonin sun amincewa wakilan jam'iyyar da su zabi wanda ransu yake so

- Akalla wakilai 4,000 ne za su kada kuri'a babban zaben da zai gudana yau Asabar, a garin Fatakwal

Gwamnoni karkashin jam'iyyar PDP sun hada kansuwa wajen nuna kin amincewaesu na arawa kowanne dan takara baya a babban taron jam'iyyar da zai gudana a yau Asabar, taron da jam'iyyar za ta zabi dan takarar shugaban kasarta a garin Fatakwal.

Majiya daba daban da suka bayyana yadda sakamakon ganawar gwamnonin da ta gudana a gidan gwamnatin jihar Rivers da ke Fatakwal sun shaidawa kamfanin jarida na Premium Times cewa gwamnonin sun bukaci wakilan jam'iyyar da su je su zabi wanda ransu yake so.

Daya daga cikin majiyar ya ce "Yanzu suka gana, kuma sun ki amincewa da nad'a wani ba tare da zabe ba," taron dai ya gudana ne da misalin karfe 12:09 na daren ranar asabar. "A yanzu wakilan na da yancin zabar wanda ransu ya ke so."

Akwai tsoron cewa gwamnonin jam'iyyar 11 na iya goyon bayan wani dan takara guda daya tilo. Duba da irin muhimmiyar rawar da gwamnonin ke takawa a harkokin jam'iyyar, masu fashin baki na ganin cewa duk wanda suka tsayar, zai iya samun nasara.

KARANTA WANNAN: Kotu ta yanke hukuncin kisa akan direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC

Da dumi dumi: Gwamnonin PDP sun rantse ba zasu goyi bayan kowanne dan takara ba
Da dumi dumi: Gwamnonin PDP sun rantse ba zasu goyi bayan kowanne dan takara ba
Asali: Twitter

Akwai gwamnoni 2 da ke takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, wanda ake ganin ba zai kyautu idan sauran gwamnonin suka mara masu baya ba.

Sai dai a yanzu da gwamnonin suka sakarwa wakilan mara, hakan ya kara armashi ga wannan babban zaben fitar da gwani, domin kuwa gaba daya yan takarar suna da ayyukan nunawa a kasa da za su sanya wakilan su zabe su.

Akalla wakilai 4,000 ne ake sa ran za su kad'a kuri'a a zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasar, a cewar jami'an jam'iyyar. Tun a jiya Laraba ne suka fara yin dafifi a garin na Fatakwal, yayin da ake sa ran isowar ragowar a ranar Asabar dinnan.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel