Yanzu-yanzu: Atiku ya lashe zaben fiddan gwanin PDP, zai yi takara da Buhari
1 - tsawon mintuna
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya lallasa dukkan sauran yan takara 11 da sukayi takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP. Ya lashe zaben da kuri'u 1653.
Sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyar PDP sun fara fitowa, zuwa yanzu, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi ya samu kuri'u 74, Kwankwaso ya samu kuri'u 158, Makarfi 74, Saraki 317
Jonah Jang —19
Datti Ahmed — 5
David Mark — 35
Tanimu Turaki — 65
Sule Lamido — 96
Attahiru Bafarawa — 48
Ibrahim Dankwambo — 111
Aminu Tambuwal: 693
Atiku Abubakar - 1653

Asali: Original
Asali: Legit.ng