APC ta kori gaba daya shuwagabannin jam'iyar na jihar Zamfara gabanin babban taronta
- Kwamitin gudanarwa na kasa, na jam'iyyar APC ya kori gaba daya shuwagabannin jam'iyyar a matakin jihar Zamfara
- Don haka, jam'iyyar ta haramtawa Gwamna Yari da korarrun shuwagabannin saka hannu a zaben jam'iyyar na jihar
- Za a gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar da 'yan majalisu a ranar Asabar, 5 zuwa Lahadi, 6 ga watan Oktoba, 2018
Kwamitin gudanarwa na kasa, na jam'iyyar APC ya kori gaba daya shuwagabannin jam'iyyar a matakin jihar Zamfara. Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa Yekini Nabena, wacce ya bayar a ranar Juma'a.
Wannan matakin na korar shuwagabannin, ya zo awanni 24 gabanin babban taron jam'iyyar na kasa da ta shirya gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta ce: "Da wannan hukuncin, dukkanin wasu shuwagabanni na jam'iyyar APC a jihar Zamfara an sallame su daga aiki. Kwamitin da hukumar gudanarwar jam'iyyar da ta kafa ne zai gudanar da zaben fitar da gwani na kujerar gwamna da sauran kujerun yan majalisu a jihar.

Asali: Depositphotos
KARANTA WANNAN: Ranar Malamai: An mayar da malamai saniyar ware a Nigeria - Masu ruwa da tsaki
"Don haka, jam'iyyar ta haramtawa gwamnan jihar Zamfara, H.E Alh. Abdul'aziz Abubakar Yari da kuma korarrun shuwagabannin saka hannu a zaben fitar da gwani na jihar da jam'iyyar za ta gudanar.
"Za a gudanar da zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar da 'yan majalisu a ranar Asabar, 5 ga watan Oktobam 2018 zuwa ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoba, 2018"
Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng