Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata

Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata

- Mr. Wahab olabamiji, ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa, saboda Tawakkaltu ta kauracewa shimfidarsa tsawon shekaru 2

- Wahab ya ce ya sha kama matar tasa tana zagayawa tana aikata zina da wasu mazan a waje

- Tawakkaltu ta amince da kotun ta raba auren, sai dai ta bayyana cewa tana hakan ne saboda zargin cewa Wahab na dauke da cutar zami

Wani magidanci ya fadi gaban wata kotun gargajiya da ke Ibadan tare da rokonta akan ta raba aurensa da matarsa saboda matar tasa ta kauracewa gadon aurensu tsawon shekaru biyu, a cikin shekaru 7 da suka shafe matsayin miji da mata.

Magidancin, Mr. Wahab olabamiji, ya bayyana gaban kotun ne inda ya bayyana bukatarsa na kotun ta warware wannan aure, saboda matarsa, Tawakkaltu, ta daina kwanciya da shi tsawon shekaru 2 duk da cewa suna zama ne a gida daya.

Wahab, wanda ke da zama a rukunun gidaje na Olopo-Meta, da ke Ibadan, ya bayyanawa kotun cewa matar tasa na sanya shi cikin mawuyacin hali, wanda har tana zagayawa bayan idonsa tana ganawa da maza.

Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata
Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa ban goyi bayan Adeleke a zaben Osun zagaye na 2 ba - Omisore

Ya ce: "Tsawon shekaru 2 da rabi kenan Tawakkaltu ke tsanantawa rayuwa ta hanyar kaurace ma shimfidar aurenmu. Haka zalika, tana aikata zina da maza a waje, wannan ba kazafi na ke mata ba, na sha kamata da kaina ba sau daya ko sau biyu ba.

"Wata matsalar da Tawakkaltu ta bullo da ita, ta tsani 'yayan matata ta farko. Bata son ganinsu ko kadan, kuma bata boye masu kiyayyarta garesu. A gaskiya bana son ci gaba da zama da ita; ina rokon kotu ta warware wannan auren da ke tsakaninmu," a rokon da Wahab ya yiwa kotu.

A nata jawabin, Tawakkaltu bata karyata ikirarin mijin nata na cewar ta kauracewa shimfidar aurensu ba, haka zalika ta amince da wannan roko na mijin akan kotu ta raba aurensu. Sai dai ta bayyana cewa tana hakan ne bisa bin dokar da asibiti ta gindaya mata.

Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata
Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn

"Ya mai shari'a, wata malamar asibiti ta bani shawarar cewa zan iya kamuwa da cutar zamani ma damar na ci gaba da amincewa Wahab yana kwana dani, saboda an kama shi yana kwanciya da wata tsohuwa wacce ke dauke da cutar.

"Malamar likitar ta ce hanya daya kawai da zan bi don hana kaina kamuwa da cutar shine in daina kwanciya da Wahab. Sannan, akasin zarginsa, tsawon shekaru 2 da rabi kenan, babu wani namiji da ya sanni a 'ya mace," Tawakkaltu ta shaidawa kotu.

Da ya ke yanke hukunci, shugaban kotun gargajiya ta Mapo a Ibadan, Mr. Ademola Odunade, a ranar Juma'a ya warware wannan aure tsakanin ma'auratan da suka shafe shekaru 7 a tare, bisa hujjar tauye hakkin aure.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel