Muryar Amurka ta sallami ma'aikatan sashen Hausa 15 saboda karbar cin hanci

Muryar Amurka ta sallami ma'aikatan sashen Hausa 15 saboda karbar cin hanci

Muryar Amurka ta sallami ma’aikatan sashen Hausa 15, saboda zargin su da ake yi da rbar kudi da ya sabawa ka’idar aiki wato cin hanci.

Daraktar Muryar Amurka Amanda Bennett ta bayyana ahakan a wani sakon imel da ta aikewa ma’aikata a ranar Alhamis, 4 ga watakn Oktoba.

Ta bayyana cewa cewa, an shaidawa hukumomin game da zargin su a cikin "watanni da suka gabata", nan da nan kuma aka kaddamar da bincike.

Muryar Amurka ta sallami ma'aikatan sashen Hausa 15 saboda karbar cin hanci
Muryar Amurka ta sallami ma'aikatan sashen Hausa 15 saboda karbar cin hanci
Asali: UGC

Tace, “yayinda doka ta hanamu bada bayani daki-daki, bayan kammala binciken ne aka dauki matakin sallamar ma’aikatan."

Amanda Bennett tace “wani gwamna ne daga daya daga cikin wadannan yankunan da Sashen Hausa ke watsa shirye-shiryensa, ya bada kudin.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jimi Agbaje ya yi nasarar samun tikitin PDP a Lagas Yanzu Yanzu: Jimi Agbaje ya yi nasarar samun tikitin PDP a Lagas

Tace an kuma kaddamar da bincike domin tantance ko an watsa wadansu shirye shirye sabili da kudi da aka karba ne, kuma idan aka tarar da haka, za a dauki mataki nan take yadda ya kamata.

Bennet tace shugabannin sassan harsunan Afrika na Muryar Amurka sun bada cikakken goyon baya yayin gudanar da binciken da kuma shawarar da aka tsayar na sallama ko kuma niyyar sallamar wadanda abin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel