Ministar Kudi tace zata kama shuwagabannin bankuna da suka bada bashi ba bisa qaida ba
- Wasu bankunan sun kama hanyar durkushewa saboda bada bashi babu lamuni
- Yawancin manyan kasar nan da sunansu kawai suke amfani su ci bashi
- Sabuwar Ministar Kudi tace zata tsarkake harkar
Sabuwar Ministar Kudi, Zainab Ahmed, tace ta kadu matuka, kan yadda taga wasu bankunan basu bin ka'idar bada bashi ta yadda sukan bada kudi ba tare da lamuni ba.

Asali: Depositphotos
Ministar, tasha alwashin kama duk wanda ya aikata haka ta mika shi kotu, sannan a kwato kadarorin jama'a dake hannunsa.
Yadda bankuna ke aiki dai shine, karbar ajiyar kudaden mutane, sai a bada bashi ga mai bukatar kudin, yaje yayi kasuwanci, sai a dawo a raba ribar, in kuma ya kasa biyan kudin, sai a bi kadarar da ya ajje kafin cin bashin, a sayar a maidowa da masu kudi kudinsu.
DUBA WANNAN: Yadda ake mutuwa don daukar hoton burgewa
To a tsari, sai mutum ya kawo takardun ajiyayyiyar kadaras, sannan a bashi bashin. Amma a Najeriya, manyan kasar nan kanyi amfani da sunansu ne kawai su amshi bashin, kuma su gagara biya, a kasa kai qarar su, tunda manyan bankin suma basu yi daidai lokacin bayar war ba..
Kwanan baya ma, sai da gwamnati ta amshe lasisin Skye Bank saboda irin wannan kaka-nikayi da bankin ya shiga, inda a 2016 sai da aka sauya mana manyan daraktoci.
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng