Saraki ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna na APC na jihar Arewa

Saraki ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna na APC na jihar Arewa

Shugaban majalisar dattawa, kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP, Bukola Saraki ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna a jam'iyyar APC na jihar Taraba, Alhaji Sani Abubakar Danladi.

Saraki ya ziyarci Jalingo ne domin ganawa da wakilan jam'iyyar PDP gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa da PDP za ta gudanar a gobe Asabar 6 ga watan Oktoba a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Dan takarar na APC na sauka a filin tashin jirage na Danbaba Suntai wasu mintuna kafin Saraki ya bar jihar.

Saraki ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna na APC na jihar Arewa
Saraki ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna na APC na jihar Arewa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: PDP za ta tursasa wa wasu 'yan takarar shugabancin kasa su janye

"Bayan Saraki ya iso jihar a jirgin sa, ya wuce kai tsaye zuwa cikin gari. Jim kadan kuma Sani Danladi ya wuce a motarsa kirar Toyota Camry 2015 zuwa daki na musamman (VIP) na hutuwar baki," inji wata shaidan ganin ido

"Bayan misalin mintuna 15, Saraki ya sake dawowa filin tashin jiragen saman kuma ya wuce dakin VIP inda Danladi ya ke yayin da sauran tawagarsa suka wuce wurin da jirginsa ya ke ajiye."

Wani majiyar ya ce an hana kowa zuwa yankin VIP din lokacin da Saraki da Danladi ke ganawa har ma'aikatan filin tashin jirgin saman ba su shiga wajen ba.

Dan takarar gwamna na APC a yanzu shine mai bawa Saraki shawara na musamman kan ayyukan na musamman.

Masu ruwa da tsaki a APC ta jihar Taraba sunyi korafi jkan zaben da aka gudanar da Danladi ya lashe inda su kayi zargin an tafka magudi sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel