Shahrarren dan majalisan nan Gudaji Kazaure ya samu nasara a zaben fidda gwani

Shahrarren dan majalisan nan Gudaji Kazaure ya samu nasara a zaben fidda gwani

Shahrarren dan majalisan nan mai wakiltan mazabar Kazaure /Roni/Gwiwa/Yankwashi a jihar Jigawa, Muhammad Gudaji Kazaure, ya lashe zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a garin Kazaure.

Shugaban zaben, Mohammed Mujaddadi, ya alanta cewa Gudaji Kazaure ya lashe zaben da kuri’u 693 yayinda mai binsa Mohammed Alhassan ya samu 372.

Shahrarren dan majalisan nan Gudaji Kazaure ya samu nasara a zaben fidda gwani
Shahrarren dan majalisan nan Gudaji Kazaure ya samu nasara a zaben fidda gwani
Asali: Facebook

Mohammed Mujaddadi ya kara da cewa Kabiru Ahmed ya samu kuri’u 84, sanna Abdullahi Mainasara wanda ya zo na karshe ya samu kuri’u 45.

Dan majalisan ya shahara da bada dariya a zauren majalisa da kuma bayyana soyayyarsa da goyon bayansa ga shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa

A bangare guda, wata shahrarriyar yar majalisa wacce ta shahara da kwazo, Nnena Ukeje, ta rasa tikitin jam’iyyar PDP yayinda aka lallasata a zaben fidda gwani a jiharta na Abiya.

Wannan abu bai yiwa yan Najeriya da dama dadi ba bisa ga irin gudunmuwar da take badawa a zauren majalisa kan abubuwan da suka shafi cigaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel