2019: PDP za ta tursasa wa wasu 'yan takarar shugabancin kasa su janye

2019: PDP za ta tursasa wa wasu 'yan takarar shugabancin kasa su janye

Shugabanin jam'iyyar PDP na kasa yau za su gana da masu neman takarar shugabancin kasa 12 na jam'iyyar domin suyi kokarin shawo kan wasu daga cikin 'yan takarar su janye gabanin babban zaben jam'iyyar da za'a fara a Port Harcourt daga gobe.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa jam'iyyar tana fargabar yadda yawan 'yan takarar zai iya kawo cikas bayan an zabi daya tak daga cikinsu wanda zai yiwa jam'iyyar takara a zaben 2019.

Hakan yasa jam'iyyar ta kira taro yau a Abuja inda za a bukaci 'yan takarar su rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da sakamakon zaben ba tare da tayar da wata rikici ba.

2019: PDP za ta tursasa wa wasu 'yan takarar shugabancin kasa su janye
2019: PDP za ta tursasa wa wasu 'yan takarar shugabancin kasa su janye
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Dan majalisar APC ya koma PDP bayan rasa tikitin takara

Za kuma a bukaci su bayyana a rubutance cewar za su marawa duk wanda ya yi nasarar baya domin jam'iyyar ta yi nasarar lashe kujerar shugbancin kasa a babban zabe mai zuwa a 2019.

A hirar da yayi da manema labarai jiya a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja, Mai magana da yawun jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya ki ya bayyana asalin makasudin kiran taron sai dai ya ce an sa ran wakilai 3,619 tare da dukkan masu neman takara a jam'iyyar za su hallarci taron.

A jiya, Legit.ng ta kawo muku cewa jam'iyyar na PDP ta yi ikirarin cewa jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) tana kokarin tarwatsa taron na jam'iyyar PDP a yunkurinta na ganin cewa jam'iyyar ta gaza fitar da dan takarar shugabancin kasa.

Sai dai ya ce hakan ba zai hana jam'iyyar ta cigaba da tsare-tsaren gudanar da taron kamar yadda ta shirya a baya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel