Zaben gwaji: Atiku ya kwala Kwankwaso, Saraki da Tambuwal da kasa a zaben fitar da gwanin PDP

Zaben gwaji: Atiku ya kwala Kwankwaso, Saraki da Tambuwal da kasa a zaben fitar da gwanin PDP

- Atiku ya kwala Kwankwaso, Saraki da Tambuwal da kasa a zaben fitar da gwanin PDP

- An gudanar da zaben gwajin ne a dandalin sada zumunta na Tuwita

A wani zaben gwaji a dandalin sada zumuntar zamani na Tuwita, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe wani dan kwarya-kwaryan zaben fitar da gwani na gwaji da aka gudanar.

Zaben gwaji: Atiku ya kwala Kwankwaso, Saraki da Tambuwal da kasa a zaben fitar da gwanin PDP
Zaben gwaji: Atiku ya kwala Kwankwaso, Saraki da Tambuwal da kasa a zaben fitar da gwanin PDP
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotuna da labarin wani dan shekara 19 da ya auri yar shekara 39 a Najeriya

A zaben wanda akawunt din jam'iyyar PDP na jihar Ribas ya gudanar, Atiku Abubakar din ya sanmu mafiya yawan kuri'un da aka kada inda ya kada shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Sanata Kwankwaso da kuma Aminu Tambuwal.

Legit.ng ta samu cewa sakamakon zaben dai ya nuna cewa Atiku ya lashe kaso 48 na kuri'un da aka kada inda Saraki ke bi masa da kaso 37 sai Kwankwaso mai kaso 11 daga karshe kuma Tambuwal da ke da kaso 4 kacal.

Haka zalika mun samu cewa zaben wanda aka gudanar cikin kwanaki 6, mutane 41,734 ne suka jefa kuri'ar su.

Duk da kasancewar wannan ba wai ainihin zabe bane, amma yakan zama wata 'yar manuniya ga yadda zaben zai iya kasancewa.

A wani labarin kuma, Shari'ar da wata kutu a garin Abuja ke yi akan Maryam Sanda - matar nan da ta kashe mijin ta a lokutan baya ta dauki wani sabon salo biyo bayan janyewar lauyoyin ta 3 dake kare ta daga shari'ar, kamar dai yadda muka samu daga majiyar mi.

Biyo bayan hakan ne kuma, haka zalika sai kotun ta sake daga shari'ar da take yi akan karar da aka shigar mata ya zuwa 24 ga watan Oktoba domin cigaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel