Wani Gwamna a Najeriya ya garkame gidan tsohon gwamnan jaharsa

Wani Gwamna a Najeriya ya garkame gidan tsohon gwamnan jaharsa

Gwamnatin jahar Oyo a karkashin umarnin gwamnan jahar, Abiola Ajimobi ta garkame gidan tsohon gwamnan Otunba Adebayo Alao-Akalada wata cibiyar binciken kimiyyar fure ta kasa dake garin Ibadan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an hukumar tattara kudaden haraji na jahar, tare da jami’an tsaro dauke da bindigu ne suka dira gidan Akala dake lamba 32 akan titin Oba Adebimpe, cikin unguwar Dugbe a garin Ibadan, inda suka garkame gidan bayan sun mika ma masu gadin gidan takardar kashedi.

KU KARANTA: An binne yayan jam’iyyar APC 5 da suka mutu a sanadiyyar rikicin jahar Zamfara

Haka zalika jami’an hukumar sun garkame kamfanin Agril Nigeria Ltd, Bevpak, Fleet, Heineman Edu Books, Mansard Insurance, Merck Phamaceuticals, Pixels Digital System, Vintage Rock Nigeria Ltd, Virgo Services Nigeria Ltd da kuma kamfanin tafiye tafiye na Wakanow.com.

Wani Gwamna a Najeriya ya garkame gidan tsohon gwamnan jaharsa
Akala da Ajimobi
Asali: UGC

Shugaban hukumar tattare kudaden haraji na jahar Oyo, Bicci Alli ya bayyana cewa kamfanonin da suka garkame sun kasance basa biya kudaden haraji tun daga shekarar 2003, inda ya kara da cewa gwamnatin jahar ta dukufa wajen tabbatar da kamfanoni sun biya harajinsu zuwa watan Yuli.

Sai dai tsohon gwamnan jahar Oyo Alao-Akala ya bayyana cewa wannan matakin da gwamnatin ta dauka akan gidansa a matsayin bita da kullin siyasa ne gwamnatin jahar ke yi masa, Akala ya bayyana haka ne ta bakin Kaakakinsa, Jeremiah Akande.

A wani labarin kuma uwar jam’iyyar APC ta yi watsi da minister sadarwar, Adebayo Shittu dake takarar zama gwamnan jahar Oyo bisa dalilin rashin yin bautan kasa na NYSC da ake bukatar kowanni dan Najeriya yayi da zarar ya kammala karatun jami’a ko HND.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel