CNN ta bankado yadda ake tursasa matan Nigeria harkar karuwanci a filin shakawar Farisa

CNN ta bankado yadda ake tursasa matan Nigeria harkar karuwanci a filin shakawar Farisa

- Kamfanin dillancin labarai na CNN ya bankado yadda ake tursasa matan Nigeria shigar harkar karuwanci a birnin Farisa

- Akan yaudari matan da cewar za su samu arziki da hutu a kasashen turai tare da yin rantsuwa a gaban boka na yi gum da bakinsu

- Idan sun isa kasar Farisa, ana kwace fasfo da komai nasu, sannan a kaisu filin shakatawa na Bois de Vincennes don yin karuwanci

Wani sabon rahoto da CNN ta fitar, ya fayyace yadda wasu matan Nigeria da aka yi safararsu daga kasar ake tursasa su shiga harkar karuwanci musamman a wani filin shakatawa da ke birnin Farisa, babban birnin kasar Faransa.

Tsawon shekaru ke nan, labarai na ta yawo a kafafen watsa labarai kan matan da ake yaudararsu wajen tara 'yan kudinsu su bayar don zuwa kasashen turai da tunanin samun alatun duniya, karshe su tsinci kawunansu a harkar karuwanci.

A rahoton da CNN ta fitar na baya bayan nan, babban filin shakatawa na Bois de Vincennes, da ke wajen gabashin Farisa, ya shahara wajen tara karuwa, 'yan caca, wanda ya zamo wajen kasuwancin mata da ke karuwanci da zaran dare ya tsala.

KARANTA WANNAN: PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa

Babban filin shakatawa na Bois de Vincennes, ya shahara wajen tara karuwai, da aka yo safarar su
Babban filin shakatawa na Bois de Vincennes, ya shahara wajen tara karuwai, da aka yo safarar su
Asali: UGC

Nadege (ba sunata na gaskiya ba), daya daga cikin matan da aka yi safararsu, wacce ta samu nasarar tserewa, ta shaidawa BBC yadda wata 'yar Nigeria, "Madam" da suka hadu a Legas ta yi mata alkawarin sama mata aikin mai bawa mutane abinci a gidan dafa abinci a kasar turai.

"Ta shaida min cewa babu arzikin da jin dadin da ba zan samu ba idan na je, amma da na isa, sai na gano kamar na fita daga tafasasshen ruwan zafi na fada na man gyada. An kawo ni Faransa daga Nigeria ina da shekaru 20, an tursasa ni shiga karuwanci akan dala 23," a cewar Nagede.

Ta ce kafin a tafi da ita da sauran 'yan matan zuwa Farisa, sai da Madam ta sanya suka yi rantsuwa a gaban boka, a cikin akwatin gawa, cewar ba zasu sanar da kowa hakan ba, wanda ya karya alkawarin kuwa zai mutu. Bayan isar su, sai matar ta kwace fasfo nasu, dama dai na bogi ne.

KARANTA WANNAN: Kungiyar Musulman jihar Oyo sun bukaci Ajimobi a samar da kotun shari'ar musulunci

CNN ta bankado yadda ake tursasa matan Nigeria harkar karuwanci a filin shakawar Farisa
CNN ta bankado yadda ake tursasa matan Nigeria harkar karuwanci a filin shakawar Farisa
Asali: UGC

Nagede ta ce ta raba gari ita da Madam dinta a lokacin da tayi ciki bayan shekara daya da zuwanta, kuma ta kuduri aniyar barin cikin, tare da gargadar mata da kauracewa zuwa kasashen turai neman abun duniya.

Bayan da ta tsere, ta ce "na zauna zaman jiran in zama mahaukaciya ko in mutu kamar yadda bokan Nigeria ya gargade mu. Ina ta tunanin ko in koma harkar karuwancin in zubar da cikin. Sai dai ban yi hakan ba, duk da cewa har yanzu bani da wata makoma, rayuwar da na yi ta lalata rayuwata ta gaba."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel