Gwamnan Kebbi ya yi kaca-kaca da zaben cikin gida na APC a jihar Imo

Gwamnan Kebbi ya yi kaca-kaca da zaben cikin gida na APC a jihar Imo

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya bayyana zaben fitar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC da aka yi a jihar Imo da sabon salo a damfara.

Da yake magana da manema labarai yau, Alhamis, bayan kammala taron wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, a Abuja.

Bayan kammala zaben fitar da dan takarar gwamna a jihar Imo, 'yan takarar kujerar su biyu; Sanata Hope Uzodinma, da surukin gwamna Richas, Uche Nwosu, kowa na murna da ikirarin shine ya yi nasara.

A yayin da shugaban kwamitin gudanar da zaben, Ahmed Gulak, ya bayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben, sakataren kwamitin, Henry Idahagbon, ya bayyana Nwosu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamnan Kebbi ya yi kaca-kaca da zaben cikin gida na APC a jihar Imo
Atiku Bagudu
Asali: UGC

Bayan wannan cakwakiya sai uwar jam'iyyar APC ta soke zaben har sai baba-ta-gani.

Bagudu ya bayyana abin da ya faru a jihar Imo da abun dariya.

"Abinda ya faru a jihar Imo za a kiransa da sabon salo na damfara a siyasance. Abun ma ya zama abin wasa, domin shi shugaban kwamitin zaben ya tafi ya bar wurin da ake kada kuri'a, daga dakinsa na Otal ya sanar da sakamakon zaben da ba ya nan aka yi," a cewar Bagudu.

DUBA WANNAN: Zaben cikin gida: Yadda aka shiryawa Kawu Sumaila gadar zare har Kabiru Gaya ya kayar da shi

A yau ne dai gwamnonin APC 9 suka gana da shugaba Buhari domin yi masa korafi a kan yadda zabukan cikin gida suka gudana a jihohinsu.

Kazalika gwamnonin sun gana da Oshiomhole domin bayyana rashin gamsuwar su da zaben cikin gida da APC ta gudanar a jihohin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel