Dandalin Kannywood: An kai wa mawaki Ado Gwanja farfaki a ofishin sa
A ranar Talatar da ta gabata ne dai wasu matasa da ba'a san ko suwaye ba da suka kai akalla 8 zuwa 10 suka kaiwa fitaccen mawakin nan kuma jarumi a masana'antar shirya fina-finai watau Ado Gwanja hari a ofishin sa.
Matasan dai kamar yadda muka samu sun kai wa mawakin wanda ke shirin zama ango a karshen wannan watan hari ne da misalin karfe 8 na dare.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Buhari ya aikawa Saraki wasika mai muhimmaci
Matasan dai wadanda ba'a gama tantance dalilin kai masa harin ba, sun je ofishin na sa ne a cikin fushi inda suka tambayi wadanda suka tadda ko mawakin yana ina amma suka yi rashin sa'a ba ya nan a lokacin.
Wannan ne ma ya sa matasan suka soma zage-zage tare da fito da muggan makamai suna fadar kalaman batanci ga mawakin tare da shan alwashin za'a taradda shi a duk inda yake suka kai masa farmaki.
Sai dai kuma majiyar mu ta tabbatar mana da cewa jama'ar dake a wurin lokacin da matasan suke kokarin aiwatar da ta'addancin su, sun far masu inda suka ci karfin su tare da kama wasu biyu daga ciki kafin daga bisani sauran su tsere.
Kawo yanzu dai, tuni muka samu cewa wadanda aka kama din an mika su a hannun 'yan sanda domin su kammala gudanar da bincike a kan su tare da daukar mataki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng