Kungiyar Musulman jihar Oyo sun bukaci Ajimobi a samar da kotun shari'ar musulunci

Kungiyar Musulman jihar Oyo sun bukaci Ajimobi a samar da kotun shari'ar musulunci

Shuwagabannin kungiyoyin da suka hada da kungiyar Muslim Ummah reshen Kudu-maso-Yamma (MUSWEN) dakuma kungiyar al'umar musulmin jihar Oyo (MUSOYS), sun yi kira ga gwamnan jihar Abiola Ajimobi da ya samar da kotun shari'ar musulunci a jihar.

Shuwagabannin kungiyoyin sun yi wannan kiran ne a wani taro na 2018/2019 don bukin murnar fannin shari'ar lardi na jihar Oyo, wanda ya gudana a babban masallacin Juma'a, da ke Oja-Oba, Ibadan, a ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN: Ta tabbata Atiku ne zai iya karawa da Buhari a 2019 - Sakamakon zaben yanar gizo

A jawabansu daban daban, Farfesa Noibi Dawud na kungiyar MUSWEN da takwaransa Mr Kunle Sanni na kungiyar MUSCOYS sun ce lokaci ya yi da ya kamata ace jihar Oyo ta shiga sahun sauran jihohi da suke amfani da kotun shari'ar musulunci.

Kungiyar Musulman jihar Oyo sun bukaci Ajimobi a samar da kotun shari'ar musulunci
Kungiyar Musulman jihar Oyo sun bukaci Ajimobi a samar da kotun shari'ar musulunci
Asali: Depositphotos

Sun bayyana cewa da yawa daga cikin musulman shiyyar Kudu-maso-Yamma sun manta da irin tarin ilimi da hikimar da su ke da ita daga shari'ar musulunci na warware matsalolin al'ummar ta hanyar shari'ar musulunci, amma yanzu lokaci ya yi da ya kamata a kaddamar da hakan.

Da ya ke maida jawabi kan wannan bukata tasu, sakataren gwamnatin jihar, Mr Olalekan Alli ya ce zai isar da wannan sakon bukatar tasu ga gwamnan jihar, a lokaci daya kuma yana mai bukatarsu akan kada su ce za su bi wasu hanyoyin karfi da yaji na ganin sun samu biyan bukatunsu.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel