Ambaliyar ruwa: Za a fuskanci karancin shinkafa a shekara mai zuwa a Nigeria - Ogbeh

Ambaliyar ruwa: Za a fuskanci karancin shinkafa a shekara mai zuwa a Nigeria - Ogbeh

- Ministan noma da bunkasa karkara, Chief Audu Ogbeh ya ce kasar zata fuskanci karancin shinkafa a 2019

- Ya ce ambaliyar ruwan ta shafi jihohin da suka shahara wajen noman shinkafa, da suka hada da Kebbi, Jigawa, Anambra da jihar Kogi

- Gwamnati ta samar da sabon irin shinkafa mai suna Faro 66 da 67 wanda baya lalacewa koda anyi ambaliya

Ministan noma da bunkasa karkara, Chief Audu Ogbeh ya ce matukar ba a dauki matakan da suka dace ba na magance yawan ambaliyar da ke afkuwa a jihohin Nigeria, to kuwa kasar zata fuskanci karancin shinkafa a 2019.

Chief Ogbeh ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da hukumar samar da irin noma ta kasa NASC da kuma babban taron baje kolin iri da ranar shiga gonar manoma na wannan shekarar ta 2018.

Ministan ya ce ambaliyar ruwan da ta shafi wasu manyan jihohi da suka shahara wajen noman shinkafa, da suka hada da Kebbi, Jigawa, Anambra da jihar Kogi, na iya haddasa karancin shinkafar a 2019 a fadin kasar ma damar ba a magance matsalar ba.

KARANTA WANNAN: Kotu ta haramtawa INEC yin kutse ga sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun

Ambaliyar ruwa: Za a fuskanci karancin shinkafa a shekara mai zuwa a Nigeria - Ogbeh
Ambaliyar ruwa: Za a fuskanci karancin shinkafa a shekara mai zuwa a Nigeria - Ogbeh
Asali: UGC

Don haka, ya shawarci manoma da su yi amfani da ruwan da ambaliyar ya tara a gonaki, wajen sake shuka shinkafar don magance karancinta a shekara mai zuwa.

Ogbeh ya ce: "Dole ne mu nemi hanyoyin da sakwanninmu za su isa kunnuwan monoma musamman wadanda suka rasa amfanin gonarsu, kamar a jihohin Jigawa, Kebbi, Anambra da Kogi, da yawa manoma a yankin sun rasa shinkafar da tsuka noma."

Ya ce: "An samar da wani sabon irin shinkafa a hukumar samar da iri ta kasa, mai suna Faro 66 da 67 wanda baya lalacewa koda anyi ambaliya, muna fatan shigar da irin ga jama'a ta yadda manoma za su shukasu a nan gaba."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel