Da dumi-dumi: Gwamnonin APC 9 na ganawa da Buhari kan Oshiomole

Da dumi-dumi: Gwamnonin APC 9 na ganawa da Buhari kan Oshiomole

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a ofishinsa dake fadar shugaban kasa Aso Villa.

Daga cikin gwamnonin da ke halarce sune gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari; gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Sauran sune gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Plateau, gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko AlMakura da gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Duk da cewan basu bayyana dalilin wannan ganawa ta gaggawa ba, ana kyautata zaton sun kai karan shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, ne kan zabubbukan fidda gwani da ke gudana a jihohinsu.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun mamaye titunan Kaduna yayinda za’a gurfanar da El-Zakzaky, da yiwuwan a bashi beli

Mun kawo muku rahoton cewa Wata sabuwar rikici ta kunno kai shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da akalla gwamnonin jam’iyyar hudu yayinda suke shirin fito na fito da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.

Gwamnonin sune: Abdulaziz Yari na jihar Zamfara; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Ibikunle Amosun na jihar Ogun. Suna rikici ne kan yunkurin da jam’iyyar keyi na baiwa wasu sanatoci tikitin kai tsaye na takara ba tare da yin zaben fid da gwani ba.

Gwamnonin sun fara zargin shugaba jam’iyyar ta shugabannin jam’iyyun ta jiha kan kokarin yi musu kama karya wajen zaben yan takara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Legit.ng Hausa zata koma LEGIT.ng Hausa, wannan babban cigaba ne

Asali: Legit.ng

Online view pixel