Yadda wani maigida ya hada baki da abokansa don yiwa matarsa fashi

Yadda wani maigida ya hada baki da abokansa don yiwa matarsa fashi

'Yan sanda sun kama wani Adewale Lukman da ake zargi da hada baki da abokansa Bidemi Fatai, Saheed Owolabi da Babatunde Ageele inda suka yiwa matarsa, Funmilayo fashin kudinta N159,000.

Punch ta ruwaito cewar mata da mijin suna zaune a Leadway Estate, Eruwen, Ikorodu a jihar Legas.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar matar, Funmilayo ta samu kwangilar gini a ranar 23 ga watan Yuli na N159,000, hakan yasa mijinta ya bata shawarar ta ajiye kudin a asusun ajiyarta na banki.

Yadda wani Maigida ya hada baki da abokansa don yiwa matarsa fashi
Yadda wani Maigida ya hada baki da abokansa don yiwa matarsa fashi
Asali: Twitter

Sai dai bayan ta isa bankin tare da mijinta, ma'aikatan bankin sun ki karbar kudin Funmilayo saboda ba tayi rajistan lambar tabbatar da asusun ajiya na BVN ba.

DUBA WANNAN: Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani

Daga nan sai matar da mijinta suka koma gida da kudin.

Punch ta gano cewar Adewale ya fadawa abokansa zancen kudin da matarsa ke dashi, hakan yasa daya daga cikin abokansa mai suna Fatai ya nufi gidan matar misalin karfe 10 na dare yana tunanin ta bar kudin a gida.

Yana cikin neman inda ta ajiye kudin ne kwatsam sai Funmilayo ta shigo gidan dauke da kudin, ance sunyi kokawa amma daga baya yafi karfinta ya kwace kudin ya gudu dashi.

Funmilayo ta kai kara wajen 'yan sanda kuma aka kamo Fatai, bayan kamashi ya fadawa 'yan sanda cewar mijin matar da sauran abokansu suka tsara yadda za'ayi fashin.

An gurfanar dasu gaban kotun majistare da ke Ikorodu kan laifin fashi sai dai dukkansu sun musunta aikata laifin.

Kotu ta bayar da belin kowannensu kan N100,000 sannan ta daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Oktoban 2011.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel