Gwamna Shettima ya lashe tikitin takarar sanata a APC
Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya mallaki tikitin takarar kujerar sanata na yankin Borno ta tsakiya karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Yayi nasara a zaben fidda gwani wanda aka gabatar a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba wanda aka sanar da sakamakon a safiyar yau Alhamis, 4 ga watan Oktoba.
Ya samu kuri’u 2,735 inda ya doge abokin takararsa Alhaji Ali Wurge wanda ya samu kuri’u biyar.

Asali: Depositphotos
Yayida yake jawabi jim kadan bayan an kaddamar das hi a matsayin mai nasara, yayi godiya ga magoya bayansa akan imani da suka yi da shi.
Sanata Babakaka Garbai wanda a yanzu shine sanata mai wakiltan Borno ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ne ya tsaya a matsayin wakilin Shettima a zaben.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa an zabi Gwamna Umaru Al-Makura a matsayin dan takarar kujeran sanata na Nasarawa ta kudu a zaben 2019 karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa
Shugaban kwamitin zaben, Ismaila Ahmed, wanda ya samu wakilcin sakataren, Abdullahi Candido ya sanar da sakamakon zaben a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba, a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.
Ahmed yace Al-Makura ya samu kuri’u 1,262 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Sanata Salisu Egyegbola, wanda ya samu kuri’u 312.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng