Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73

Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73

- Akalla mutane 72 da suka hada da mata biyu ne rundunar soji ta cafke bayan zarginsu da sa hannu a rikicin da ya barke a Jos

- Haka zalika, rundunar ta musamman ta karyata wata jita-jita da ke yawo a kafofin watsa labarai na cewar an samu sojojin bogi a garin Jos

- Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya zargi masu madafun iko da kuma dattawan jihar Jos na kunna wutar rikicin da ta tashi a jihar

Akalla mutane 72 da suka hada da mata biyu ne rundunar soji ta cafke bayan zarginsu da sa hannu a rikicin da ya barke a Jos, babban birnin jihar Filato. Hadakar rundunar soji ta musamman, mai taken 'ofireshen Safe Haven' ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Haka zalika, rundunar ta musamman ta karyata wata jita-jita da ke yawo a kafofin watsa labarai na cewar an samu sojojin bogi a garin Jos, tana mai cewa, "Babu wani sojan bogi da ke bi gida-gida. Dirar mikiyar da sojoji suka yiwa yankin tare da dakile rikicin ya sanya 'yan ta'addan da suka haddasa rikicin ganin laifin soji."

Rundunar ta OPSH ta ce: "Kamar yadda kuke kallonsu a nan, 'yan ta'adda ne sanye da bakaken kaya, sune kuma aka cafke da sa hannu a rikicin, amma ba sojoji bane."

KARANTA WANNAN: Tsufana ba zai iya barina jure rashin d'ana ba - Mahaifiyar Manjo Janar Alkali

Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73
Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73
Asali: Twitter

Kwamandan rundunar OPSH, Manjo-Janar Augustine Agunde, a lokacin da ya ke gabatar da wasu 'yan ta'adda 27 a garin Jos, a yammacin ranar Alhamsi, ya bayyana cewa duk da an cafke mutane 72, zuwa yanzu 30 ne daga cikinsu suka amsa laifin da ake zarginsu da shi.

A yayin da ya ke Allah-wadai da halin ko in kula da masu madafun iko da kuma dattawa suka nuna akan abubuwan da ke faruwa a jihar, ya yi gargadin cewa rundunar ba zata sassautawa kowa ba ma damar aka sake kaiwa dakarunta hari.

"Amma abun takaicin shine su (dattawa da masu madafun iko) sun yi shiru akan hakan. Idan har suna son kawo karshen wannan rikicin da kisan gillar da akewa mutanen da basu ji ba basu gani ba, za su iya yin hakan a cikin kiftawar ido," a cewar Agundu.

KARANTA WANNAN: Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno

Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73
Rikicin Jos: Buratai ya zargi masu madafun iko da haddasa rikicin bayan cafke mutane 73
Asali: UGC

Haka zalika Legit.ng ta ruwaito maku cewa hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya zargi masu madafun iko da kuma dattawan jihar Jos na kunna wutar rikicin da ta tashi a jihar.

Buratai wanda ya samu wakilcin Agundu, ya bayyana hakan a ranar Labarai, a lokacin bizne sojoji uku da aka kashe a karamar hukumar Barikin Ladi, da aka kashe su a ranar 6 ga watan Satumba, 2018.

A cewarsa, kalaman dattawan da masu madafun iko ne suka harzuka zukatan matasan da suka hadda rikici a Jos, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama wadanda basu ji ba basu gani ba, wasun su ma matafiya ne da hanya ta bi da su a yankin.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel