Idan ajali ya yi kira: Mutane 6 sun mutu, motoci sun kone a wani hatsarin tankar dakon mai

Idan ajali ya yi kira: Mutane 6 sun mutu, motoci sun kone a wani hatsarin tankar dakon mai

Wata wuta da ta kama ganga-ganga bayan wata tankar dakon man fetur ta yi bindiga a kan babban hanyar Akure-Owo-Benin a jihar Ondo ta haddasa asarar rayuka da dukiya mai yawa.

Hatsarin ya faru ne da yammacin yau, Laraba, bayan tankar ta kubuce daga kan hanya tare da tsiyayar da litar man fetur 33,00 da take dauke da shi.

Duk ba a fitar da alkaluman asarar rayukan da aka samu ba a hukumance, shaidar gani da ido ya sanar da jaridar SaharaReporters cewar a kalla mutane 6 sun rasa ransu yayin da motoci 5 suka kone kurmus.

Wurin da hatsarin ya afku bashi da nisa da babban gidan man fetur na NNPC na garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Wani shaidar gani da ido ya alakanta afkuwar hatsarin da rashin hakurin direban tankar dakon man.

Daya daga cikin shaidar gani ya ido ya shaidawa wakilin sahara cewar, “hatsarin ya faru ne bayan motar dakon man ta kwace daga hannun direbanta sannan ta tsallaka hannun da ba a kansa ta ke ba. Hatsarin ya ritsa da Jama’a da ababen hawa da dama dake kan hannun da motar ta tsallaka.

“Duk da bamu da alkaluman adadin mutanen da suka mutu, muna da tabbacin cewar mutanen dake cikin wata mota kirar Toyota da tankar ta doka sun kone kurmus.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel