Kabilar Ibo sunce dole a basu kujerar mataimakin shugaban kasa a badi

Kabilar Ibo sunce dole a basu kujerar mataimakin shugaban kasa a badi

- An mayar da kabilar Ibo saniyar ware tun bayan yakin basasa

- Yanzu kam sunce lokaci ne da zasu dandana mulki

- Tun Alex Ekueme basu kara rike babbar kujera ba

Kabilar Ibo sunce dole a basu kujerar mataimakin shugaban kasa a badi
Kabilar Ibo sunce dole a basu kujerar mataimakin shugaban kasa a badi
Asali: Facebook

Kabilar Ibo, a wannan karon, sunce allan katafur sai an dama dasu a zaben 2019 mai kamawa, inda suka ce kujera lamba biyu suke nema, sai dai ba'a san ko a PDP suke nufi ba ko a APC.

An maida kabilar saniyar ware ne, tun bayan yakin basasa, saidai daga baya an sulhunta inda har Alex Ekweme yayi mataimaki ga Shagari.

A yanzu dai, akwai manyan 'yan siyasa dake kudu masu bakin fada aji a Arewa, a APC, kamar su Rochas Okorocha da Uzor Kalu, sai dai babu su a tikitin APC.

DUBA WANNAN: An rataye ta kan wai ta kashe mijinta

Ana sa rai, Atiku Abubakar zai dauko wani daga kabilar don ya mara masa baya a matsayin mataimaki a jam'iyyar PDP, sai dai a cikin gida akwai masu neman kujerar suma, kamar Tambawal, Dankwambo, Makarfi, da Kwankwaso.

Wasu samari masu kokarin balla Najeriya, watau IPOB, sun dan tada kayar baya a baya, bayan da suka dauka ta shugaba Buhari ta qare lokacin yana rashin Lafiya.

Sai dai, yana dawowa ya sanya taakalmi ya murkushe su, a wani shiri na Atisaye da soji suka kira rawar macijiya.

Babu dai wanda ya san ko Kabilar, zasu sami abinda suka zo nema Abuja ko a'a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel