An gano ashe kungiyar Osama bin Laden ta al-qaida ce ta baiwa Boko Haram kudi har $250,000 a 2019

An gano ashe kungiyar Osama bin Laden ta al-qaida ce ta baiwa Boko Haram kudi har $250,000 a 2019

- Tun bayan mubayi'ar Boko Haram ga ISIS, an sami wasikunsu da bayanai

- Ashe yuro 200,000 Usama ya baiwa Shekau don a kashe mutane a Najeriya

- An rabe biyu a tsakanin Boko Haram ta Shekau da ta dan Muhammad Yusuf

Yaki da Ta'addanci: Musayar wasika tsakanin Boko Haram da IS, ga kadan daga ciki
Yaki da Ta'addanci: Musayar wasika tsakanin Boko Haram da IS, ga kadan daga ciki
Asali: Twitter

A wani littafi da shugaban Boko Haram bangaren ISWA, wanda suke kira Albarnawy, dan gidan Muhammad Yusuf, ya rubuta da Larabci, wanda muka samu fassararsa da turanci, mun tsakuro muku kadan daga cikin irin yadda Boko Haram ke aikinta na kisan gilla da cin zali.

A littafin, Albarnawy, ya zayyana yadda bayan kashe mahaifinsa, suka shiga rudani, inda daga baya kwamandojin da mahaifinsa ya baiwa tutar jihadi, suka nada Abubakar Shekau a matsayin khalifansu, a kokarinsu na yin kamanceceniya da yadda Sayyadi Abubakar wai ya gaji annabi bayan wafatinsa.

Boko Haram, wadda ita ma take kokarin sai ta kafa daular Islama a Najeriya, ta bige da kashe mutane ciki har da musulmai, karkashin mulkin Abubakar Shekau, wanda wai ashe cewa yayi tunda Allah ma ya halakar da garuruwan da ake kafirci gaba dayansu, kamar su mutanen Ludu, Adawa da Samudawa, to kuwa wai ya halasta a kone gari baki daya koda da mata da yara, inda a littafin har aka yanko batun Shekau yana cewa: "Ko sanda aka kifar da garin Adawa zaku ce min babu mata da yara da tsofi? Ku kashe! In anje lahira ni Allah zai tambaya!:

DUBA WANNAN: Zunubin Ambode

Su dai mabiya da suka ga abin yayi yawa, sun koma kai karar Shekau wurin alqaida wadda ke aiki a yanki Sahara, inda suka je karbar kudi a 2009, har Yuro 200,00, bayan shalkwatar kungiyar ta duniya ta bi diddigi kan irin aikin nasu, da kisan mutanensu da gwamnati tayi, amma tace agaji ne kar su fara yaki da gwamnati sai an shirya, Sai an aiko musu mujahidai zuwa cikin Najeriyar, amma ita kuwa Boko Haram tayi gaban kanta ta fara.

A littafin, Albarnnawi ya kuma ce sun karbi makamai daga Alkaida a Mali wadanda ita kuma ta samo su daga Mauritania, bayan wani hari da takai na samame cikin kasar, sannan wasunsu sun sami training a Somalia da Mali.

A cikin wasikun da suka yi ta musaya dai, kafin, da bayan sun kwaci garuruwa a yankin arewa maso gabas, daga 2012 zuwa 2014, sun bayyana yadda Shekau ya koma kashe kwamandojinsa da yake zargi da hana shi 'ghanima', ko kuma in yaga sun fara yin karfi.

Albarnawy dai, ya rubuta wa Al-Baghdadi takarda, inda ya tona irin ta'asar da suka tafka karkashin Shekau, bayan ISIL din sun kafa tasu daular a Siriya, ita kuwa ISIL ta sauke Shekau bayan da yayi mata mubayi'a, ta dora bangaren albarnawy, wanda shi kuma shekau yace sai ya halaka su don sunyi ridda suma.

A karshe, bangaren Albarnawy, sun aika takardar tambaya kan wai ya halasta su kashe yara a makarantu, da kuma kama yaran mutane mata don bautarwa, da ma wai ko ya halasta su kashe wanda yace duniya a dunkule take?

Amsar da suka samu, wadda wani Al-Tamimi ya bayar, jim kadan kafin harin Amurka ya hallaka shi, ya tabbatar musu cewa zasu iya kashe yara a makarantar da soji suka sanya kusa da bariki, ya kuma ce musu bautar wa zasu iya yi, amma banda yaran musulmi, sai dai na Kirista, kuma bai halasta su kashe mutane a masallatai ba, sai dai coci.

Al-Tamimi, ya kuma rufe da basu fatawar cewa ai duniya an riga an gane cewa a dunkule take ashe, don haka su bar kashe mutane don sun ce hakan, su maida hankali wajen kashe soja, da masu bin wasu addinan.

Yanzu dai, Boko Haram mai suna ISWA, ta Albarnawy, da wannan manjaha take aiki, a yankin arewacin Borno da tafkin Chadi, su kuma su Shekau suna Sambisa da Sauran kudancin Borno.

Kungiyoyin ISIS da Boko Haram dai, duk duniya ta tabbatar kungiyoyin ta'addanci ne marasa tausayi, masu kokarin sai sun zub da jinanen mutane.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel