Karya ne babu wani shiri na kara kudin makarantun jami’a – Gwamnatin tarayya

Karya ne babu wani shiri na kara kudin makarantun jami’a – Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta karyata rade-radi cewa ta amince da karin kudin jami’an Najeriya zuwa N350,000

- Babban sataren ma'aikatar ilimi ne ya saar da hakan

- Ya kuma bukaci al'umman kasar da ukwantar da hankulansu kan lamarin

Ma’aikatar ilimi na tarayy a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba tayi watsi da labarin dake tashe musamman a shafukan zumunta na cewa gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin jami’an Najeriya zuwa N350,000.

Karya ne babu wani shiri na kara kudin makarantun jami’a – Gwamnatin tarayya
Karya ne babu wani shiri na kara kudin makarantun jami’a – Gwamnatin tarayya
Asali: Depositphotos

Mista Sonny Echno, sakataren din-din-din na ma’aikatar ya bayyana hakan a Abuja.

Echono wanda yace gwamnatin tarayya bata kowani shiri na kara kudin makaranta ya bukaci ýan Najeriya da su kwantar da hankulansu akan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kano: Shekarau da wasu 2 sun yi nasarar samun tikitin majalisar dattawa a APC

Da farko dai mun ji cewa ASUU, kungiyar malaman makarantun gaba da sakandare ta kasa a jami'o'in kasar nan, ta shafe shekaru kusan 40 tana gwara wa da gwamnati, a yaje-yajen aiki don neman gwamnati ta baiwa ilimin boko kulawar da ta kamata.

A wannan karon, bayan da aka ito daga dakin sulhu, ASUU ta tona yadda gwamnatin APC ke kokarin maida karatun boko na kudi tsababa.

Dr. Ade Adejumo, mai kula da ofishin kungiyar na shiyyar yamma a kudancin Najeriya, shi ya bayyana hakan inda yace bayan zantawarsu da gwamnati a lokacin sulhun yajin aikin kwadago ne gwamnatin tarayyar ta fadi haka.

A cewarsa; "karin kudin makaranta zuwa N350,000 zai ruguza tsarin kwadago na jami'ar, kuma wannan dalilin ne yasa muka ice daga yarjejeniyar da muke kai a wannan karon."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel