2019: Jamilu Gwamna, Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC

2019: Jamilu Gwamna, Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC

- Jamil Isyaku Gwamna, dan takarar gwamnan jihar Gombe a jam'iyyar PDP ya koma APC

- Ya bayyana cewar ya yanke shawarar komawa jam'iyyar APC ne saboda jama'ar sa sun nuna bukatar son ya yi hakan

- Da yake jawabi bayan ya rasa tikitin takara a PDP a zaben cikin gida da aka yi, gwamna ya ce ya fita ne saboda babu adalci a cikin jam'iyyar

A jiya, Talata, 2 ga watan Oktoba, ne dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam'iyyar PDP, Jamil Isyaku Gwamna, ya bayyana ficewarsa daga PDP tare da sanar da komawarsa jam'iyyar APC.

Tun da fari Gwamna ya yi watsi tare da nuna kin amincewarsa da sakamakon zaben cikin gida da Sanata Bayero Nafada ya yi nasarar lashewa, yana mai bayyana cewar ba a yi masa adalci ba a zaben.

Jaridar Leadership ta rawaito Gwamna na cewar tun shekarar 2007 yake wahala da dawainiya da jam'iyyar PDP amma yanzu dole ya bar ta duk da wahalar da ya sha wajen kafa ta.

2019: Jamilu Gwamna, Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC
Jamilu Gwamna
Asali: Depositphotos

Kazalika ya bayyana cewar ba shine ya yanke shawarar barin PDP ba, magoya bayansa ne suka nemi ya yi hakan.

"Ba wai ina son zama gwamna don biyan bukatar kai na bane sai don jama'a, amma bayan jam'iyyar PDP ta yi mana rashin adalci sai jama'a ta suka nemi na bar ta domin komawa inda zai cigaba da gwagwarmaya domin kwato hakkin jama'a daga hannun azzalumai.

DUBA WANNAN: Ambode ya rungumi kaddara, ya taya mutumin da ya kayar da shi zabe murna

"Bayan tuntubar magoya baya na, mun yanke shawarar komawa jam'iyyar APC tare da hada kai da masoya son cigaban jihar Gombe domin tabbatar da samun nasarar shugaba Buhari, a matakin kasa, da Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan Gombe," a cewar Gwamna.

Sanata Bayero Nafada ne ya yi nasarar lashe zaben cikin gida a matakin gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Gombe da adadin kuri'u 1,104 yayin da Gwamna ya zo na biyu da adadin kuri'u 147.

Sai dai gwamna ya yi watsi da sakamakon zaben tare da bayyana cewar ba shine sakamakon zabe na gaskiya da daliget suka yi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel