Babu mamaki Shehu Sani, La’ah da Hunkuyi su koma Majalisar Dattawa

Babu mamaki Shehu Sani, La’ah da Hunkuyi su koma Majalisar Dattawa

Mun samu labari cewa Sanatoci 3 da Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya tsinewa albarka kwanakin baya su na neman komawa Majalisar Dattawan Najeriya a 2019.

Babu mamaki Shehu Sani, La’ah da Hunkuyi su koma Majalisar Dattawa
Kwanaki Gwamna El-Rufai yayi Sanatocin Kaduna ruwan tsinuwa
Asali: Twitter

‘Yan Majalisar da ke wakiltar Kaduna sun gamu da fushin Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufai inda ya tsine masu ta-tas bayan sun yi kutun-kutun wajen hana Kaduna karbo wasu bashin Dalolin kudi da Gwamnan yake so yayi ayyuka a Jihar.

Rigimar da ta shiga tsakanin Sanatocin da Gwamnan ne ta sa Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP. Sai dai da alamu yanzu Hunkuyi ya samu tikitin komawa Sanata bayan ya rasa takarar Gwamna a PDP.

Haka kuma kun ji cewa Shehu Sani wanda shi ne Sanatan Kaduna ta tsakiya zai yi takara a 2019 babu hamayya a APC. APC ta dauki tikitin Sanata ta mikawa Shehu Sani a sama ganin cewa yana cikin wadanda ba su sauya sheka daga APC ba.

KU KARANTA: Yaron Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

Shi ma dai Sanatan Kudancin Kaduna watau Danjuma Laah wanda dama tun can ‘Dan PDP ne ya samu lashe zaben fitar da gwani da aka yi. Idan Laah yayi nasara, kusan shi ne zai zama na farko da ya zarce a kujerar Sanatan wannan Yankin.

Sanata Danjuma Laah zai yi takara ne da watakila Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Barnabas Bala Bentex ko kuma Zagi Caleb. Sulaiman Hunkuyi kuma zai buga ne da Kwamishina Abdu Kwari a zaben Sanata na Yankin Arewacin Kaduna.

Jiya kun ji cewa Kaduna ta rikice bayan APC ta ba Shehu Sani tikitin Sanata a sama inda manyan na-kusa da Gwamna su kayi zugum bayan Uwar Jam’iyyar APC ta ba Shehu Sani tikitin 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel