Rikici ya barke a PDP a Kano bayan Kwankwaso ya yi zaben dan takara a gidansa

Rikici ya barke a PDP a Kano bayan Kwankwaso ya yi zaben dan takara a gidansa

Shugaban jam'iyyar PDP a Kano, Masa'ud El-jubrin Doguwa, ya yi watsi da sakamakon zaben fitar da dan takarar gwamna da tsagen Kwankwasiyya ya yi a gidan tsohon gwamna, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Da yake magana a yau, Talata, a madadin ragowar 'yan takarar kujeru daban-daban a jihar Kano, Doguwa ya bayyana zaben da aka yi a gidan Kwankwaso da cewar haramtacce ne da bashi da matsuguni a tsarin siyasa balle dokar jam'iyya.

Kazalika ya zargi uwar jam'iyyar PDP ta kasa da bin tsarin mutum daya kacal duk da kasancewar sune suka rike jam'iyyar a matakin jiha lokacin da kusan dukkan jiga-jigan 'ya'yanta suka fice.

Doguwa ya kalubanci uwar jam'iyyar PDP da ta zama mai adalci ga dukkan 'yan jam'iyyar da suka sayi fam din takara ta hanyar gudanar da zabe na adalci da kowa zai gamsu da sakamakon sa.

Rikici ya barke a PDP a Kano bayan Kwankwaso ya yi zaben dan takara a gidansa
'Yan takarar Kwankwaso
Asali: Twitter

"An saka dukkan ragowar 'yan takara a cikin rudani, musamman dangane da makomar zabukan fitar da 'yan takarar kujerun majalisar tarayya da ta jiha da za a yi ranakun Laraba da Alhamis mai zuwa.

"Abun takaici ne cewar mutumin da yake bako a cikin jam'iyya zai fito ya shaidawa duniya cewar ya gudanar da zaben fitar da dan takara a gidansa kuma surukinsa ne ya yi nasara a zaben da babu wani dan takara da ya san an yi," a cewar Doguwa.

Sannan ya kara da cewa, "babu zaben da aka yi a Kano domin tuni kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP ya dakatar da zaben fitar da dan takarar gwamna a jihohin Kano, Imo da Legas.

DUBA WANNAN: APC ta soke takarar Suleiman Abba, tsohon shugaban rundunar 'yan sanda

"Duk wanda ya gudanar da zabe a wannan yanayi to tabbas wasan kwaikwayo kawai ya tsara domin ba zamu yarda ba kuma ba zamu goyi bayan son rai da rashin ganin girman jama'a da doka ba."

A kalla kimanin mutum 7 ne suka sayi fam din takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP.

Ganin yadda tsagin Kwankwasiyya ke da daurin gindi a wurin uwar jam'iyya, tuni wasu daga cikin 'yan takarar sun fara tunanin nemawa kansu mafita.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar wasu daga cikin 'yan takarar zasu fita daga jam'iyyar PDP ko kuma su cigaba da zama cikinta domin su dauki fansar abinda aka yi masu a zaben duk gari da za a yi a shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel