Tsawa ta hallaka shanaye 23 a Ekiti, mamalakin Bafulatanin da ibti’in ya afkamawa yayi tsokaci

Tsawa ta hallaka shanaye 23 a Ekiti, mamalakin Bafulatanin da ibti’in ya afkamawa yayi tsokaci

Akalla shanaye 23 ne suka halaka sanadiyar wata tsawa a jihar Ekiti. Tsawar ta biyo bayan rowan sama da aka zuba kamar dabakin kwarya a yankunan jihar yan kwanaki biyu da suka gabata.

Lamarin wanda ya afku a yanin Okeowa Eluju, wani yankin gona dake Iloro-Ekti, karamar hukumar Ijero dake jihar, ya haifar da rudn a tsakanin mazauna yankin.

Yayinda yake tabbatar da lamarin, wani Makiyayi Bafulatani kuma mammalakin shanayen yace ya shiga firgici kan lamarin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Kadiriya bayyana lamarin a matsayin mai ban al’ajabi.

Tsawa ta hallaka shanaye 23 a Ekiti, mamalakin Bafulatanin da ibti’in ya afkamawa yayi tsokaci
Tsawa ta hallaka shanaye 23 a Ekiti, mamalakin Bafulatanin da ibti’in ya afkamawa yayi tsokaci
Asali: UGC

“Na je gona bayan zuba rowan sama da y kwashi tsawon kimani sa’o’i shida a safiyar ranar Litinin, kawai sai na tarar da shanaye na 23 sun mutu.

“Bayan na lura da kyau, sai a gano cewa babu wani alamu na rauni a jikins. Na yarda cewa Allah ne ya kaddar domin banyi fada da kowa ba kuma banyi ma kowa laifi ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: An matsawa yan takara lamba don su janyewa surikin Buhari

Kadiri yace bai taba fuskantar haka ba shekau 35 da ya kwashe yana sana’ar.

Shugaban garin, wanda ya tabbatar da lamari ya bayyana wanda ibtila’in ya afkamawa a matsayin salihi wanda ke son zaman lafiya.

Ya bayyana lamarin a matsayin mai ban al’ajabi a garin, yayi kira ga gwamnati da manyan masu fada a ji da su tallafawa mkiyayin domin dawo da kasuwancinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel