Yadda wani tsoho mai shekaru 75 ya gamu da ajalinsa a hannun matashi mai shekaru 23

Yadda wani tsoho mai shekaru 75 ya gamu da ajalinsa a hannun matashi mai shekaru 23

Wani matashi mai shekaru ashirin da uku, Olatunji Julius ya hau dokin zuciya inda ya kashe wani dattijo mai shekaru saba’in da biyar, Pa Isaac Durojaiye bayan ya yi masa fashin kudi naira dubu uku, inji rahoton jaridar Daily trust.

KU KARANTA: Sama da daliban firamari dubu dari uku sun samu tagomashin Buhari a sakkwato

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba a unguwar Imesi-Ile dake cikin karamar hukumar Obokun na jahar Osuna, kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar, Fimihan Adeoye ya bayyana.

Kwamishinan ya sanar da haka ne a ranar Talata a lokacin da yake bayyana ma manema labaru wannan matashi mara Imani a shelkwatar yansandan jahar, inda yace matashin ya saci kudi naira dubu uku, katukan waya, da lita 25 da manj a, sa’annan ya tsere zuwa Ekiti.

Sai dai abinka da Yansandan Najeriya da shahara wajen kwarewa da sanin makaman aiki, sai suka bi shi har jahar Ekiti, suka yi ram da shi, kuma tuni ya amsa dukkanin laifukan da ake zarginsa dasu.

Da yake karin haske kan zarge zargen da ake yi masa, Julius ya tabbatar da kashe dattijon, sa’annan ya tabbatar da satar kudi naira dubu uku dage hannunsa, tare da katukan waya da jarkan man ja. Sai dai yace bai yi nufin kashe dattijon ba, toh amma ya ga fuskarsa kuma ya gane shi.

“Tamkar Uba haka mutumin yake a wajena, kai zan iya cewa ma mahaifina ne, saboda yana min alheri, amma a ranar da na shiga dakinsa sai na sace masa kudi naira dubu uku, kuma dama yana sayar da katukan waya, nan ma na saci na naira dubu uku, da kuma jarkar manja.

“Gaskiya ban yi niyyar kasheshi ba, bani da wata hujjar kasheshi, amma dole ta sa na kasheshi saboda ya riga ya ga fuskata, kuma ya ganeni sarai, don haka babu yadda za’ayi na barshi, haka ta sa na kasheshi don kada a kamani.” Inji Julius.

Daga karshe kwamishinan Yansandan jahar yace doka zata yi aiki akan Julius, amma da zarar sun kammala bincike akansa zasu mika shi gana kuliya manta sabo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel