Bolaji Abdullahi, Ibeto, da Hunkuyi sun rasa tikiti a Jam'iyyar PDP

Bolaji Abdullahi, Ibeto, da Hunkuyi sun rasa tikiti a Jam'iyyar PDP

Yanzu haka dai wasu manyan 'Yan siyasa da su ka sauya sheka domin su samu takara a 2019 sun yi asara. Irin su Bolaji Abdullahi, Ambasada Musa Ibeto, da Sanata Suleiman Othman Hunkuyi sun rasa tikitin Jam'iyyar PDP bayan sun bar APC.

Bolaji Abdullahi, Ibeto, da Hunkuyi sun rasa tikiti a Jam'iyyar PDP
Bolaji Abdullahi ya gaza samun tikitin takarar Gwamnan Kwara a PDP
Asali: UGC

Ga cikakken bayanin 'Yan siyasan da su ka tashi biyu-babu kawo yanzu:

1. Bolaji Abdullahi

Tsohon Minista Bolaji Abdullahi ya dade yana tare da Bukola Saraki. Bayan Saraki ya sauya sheka ma dai Bolaji Abdullahi ya bar mukamin sa mai tsoka a APC inda ya sa rai zai yi takarar Gwamnan Kwara a 2019. Sai dai yanzu PDP ta hana Abdullahi tikiti ta kuwa tsaida Hon. Rasaq Atunwa.

KU KARANTA: Ana zaben fitar da gwani na Gwamnan APC a Legas

2. Musa Ibeto

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara Musa Ibeto ya ajiye mukamin sa na Jakadan Najeriya a Kasar Afrika ta Kudu ya kuma bar APC ya dawo PDP domin yayi takarar Gwamnan Neja. Yanzu dai PDP ba ta ba Ibeto tikiti ba. Alhaji Ummaru Muhammad Nasko ne ya samu tikitin PDP.

3. Sulaiman Hunkuyi

Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi yana cikin 'Yan Majalisar da su ka bar APC zuwa PDP kwanaki. Sulaiman Hunkuyi ya nemi takarar kujerar Gwamna a PDP inda ya sha kasa a hannun Isa Ashiru Kudan. Sanatan na Arewacin Jihar Kaduna ya zo na biyu ne a zaben da aka yi shekaran jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel