Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa

Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito za ku ji cewa, tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sanya masu fada aji kuma rike da madafan iko na kasar na ke ma sa adawa.

Manemin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP ya bayyana cewa, manyan kasar nan masu rike da madafan iko na kulla tuggun adawa da shi a sakamakon tsarkakakkiyar zuciya da ya ke da ita.

Atiku ya bayyana cewa, jiga-jigan kasar nan na fargaba a kansa dangane da yadda yake da kafuwa kan akida da ba bu wanda zai juyawa shi matukar yana bisa turba ta daidai muddin ya zamto shugaban kasar nan ta Najeriya.

Turakin na Adamawa ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai cikin wani taro da wata kungiyar hadin kai ta gudanar a daren ranar Lahadin da ta gabata a can birnin tarayya na Abuja.

Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa
Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa
Asali: Depositphotos

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, jiga-jigan kasar nan musamman masu rike da madafan iko da fada a ji na kasar nan na fargabar kasancewar sa shugaban kasar nan sakamakon akidarsa ta kafuwa kan akida da ba bu wanda zai juya sa son ran sa.

KARANTA KUMA: Jerin Gwanayen Takara na jam'iyyar PDP da APC da aka tsayar a jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Benuwe, Filato

A sanadiyar haka Atiku yake kira ga al'ummar kasar nan akan su yi watsi da wannan adawa tare da kwadaitar da su kan irin akidarsa da za ta fidda kasar nan zuwa tudun tsira musamman ta fuskar ceto tattalin arzikin kasar nan da a cewarsa shugaban kasa Muhammadu Buhari gurbata shi.

Ya kara da cewa, a halin yanzu Najeiya na da muradin shugaban kasa da zai samar da ayyukan yi musamman ga Matasa domin kawar da zaman kashe wando mai janyo koma baya na ci gaban tattalin arziki.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel