An kuma: Gingimari ta kama da wuta a Legas, ta kar jama'a

An kuma: Gingimari ta kama da wuta a Legas, ta kar jama'a

- Babbar motar mai ta fashe da safen nan a kusa da ofishin DSS da barikin Ojo a kan babbar hanyar Badagry

- Fashewar ta ya jawo mummunar gobara da ta hadiye ababen hawa da rayuka

- Mutanen da suka kokarin fita daga ababen hawa don tseratar da rayukan su, sun samu raunuka

An kuma: Gingimari ta kama da wuta a Legas, ta kar jama'a
An kuma: Gingimari ta kama da wuta a Legas, ta kar jama'a
Asali: Depositphotos

Wata babbar motar mai ta fashe tare da tashi da gobara a kusa da ofishin DSS da barikin Ojo dake kan babban titin Badagry a jihar Legas.

Majiyar mu ta ruwaito cewa motar ta fadi ne sanadin Lalacewar titin, inda man da ta dauko ya malale akan titin. Wanda hakan ya jawo mummunar gobara.

Gobarar ta lashe ababen hawa da rayukan mutane.

Ganau ba jiyau ba yace al'amarin ya faru ne da karfe 6:45 na safe, inda rayuka da ababen hawa suka kone.

Mutanen da suka yunkurin fita daga ababen hawa don tseratar rayukan su, sun samu munanan raunika.

DUBA WANNAN: Na gama aiki a Senate - mai Silverbird

A lokacin da majiyar mu ta isa gurin, ma'aikatan kashe gobara na Gwamnatin tarayya tare da ma'aikatan cibiyar aiyukan gaggawa na jihar Legas basu riga sun hallara ba. Hayaki na ta tashi daga ababen hawan dake ci da wuta.

Hatsarin yayi sanadiyyar cushewar titi, a yayin da masu ababen hawa dake tahowa daga Mile 2 suka koma bin titin Tedi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel