Rikicin Ambode da APC a Legas: Buhari ya gana da Tinubu da Akande

Rikicin Ambode da APC a Legas: Buhari ya gana da Tinubu da Akande

A kokarin warware rikicin da ya dabaibaye takarar gwamna Ambode na jihar Legas a APC, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawar sirri da yammacin yau, Litinin, da jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da kuma kuma shugaban riko na farko a jam’iyyar, Bisi Akande.

Duk da ganawar ta sirri ce, majiyar mu ta sanar da mu cewar ganawar na da nasaba da matsalar da gwamna Ambode ke fuskanta da Tinubu a kokarinsa na samun tikitin takara karkashin APC a karo na biyu.

Majiyar mu a fadar shugaban kasa ta kyara mana cewar shugaba Buhari na kokarin ganin an warware sabanin dake tsakanin Ambode da Tinubu domin samun hadin kan jam’iyyar APC a jihar Legas. Wata majiyar ta bayyana cewar Buhari na da ra’ayin a bar Ambode ya sake yin takara saboda irin kokarin day a yi ta fuskar shimfida aiyukan raya kasa a shekaru kusan hudu da ya yi a karagar mulki.

Rikicin Ambode da APC a Legas: Buhari ya gana da Tinubu da Akande
Ambode da Tinubu
Asali: Depositphotos

Sai dai babu tabbacin ko Tinubu ya yi na’am da wannan ra’ayi na shugaba Buhari, musamman ganin cewar tuni ya bayyana goyon bayansa ga Babajide Sanwa-Olu, abokin hamayyar Ambode.

DUBA WANNAN: Masu gudu sun dawo: Bala Kaura, tsohon ministan Abuja ya zama dan takarar gwamna a PDP

A ranar Asabar ne 'yan majalisar jihar Legas suka juya wa gwamna Akinwumi Ambode baya yayin da 36 cikin 40 na mambobin suka marawa Babajide Sanwo-Olu baya a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a zaben 2019.

'Yan majalisan sun bayyana matsayarsu ne bayan wata taro da su kayi a jiya, Asabar, karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, inda dukkan 'yan majalisar suka sanya hannu a takarda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel