Allahu Akbar: Yadda Marigayi Baba Ari ya karkatar da jirgin sa daga cikin mutane kafin mutuwar sa

Allahu Akbar: Yadda Marigayi Baba Ari ya karkatar da jirgin sa daga cikin mutane kafin mutuwar sa

Majiyar mu ta sirri a rundunar sojojin saman Najeriya ta labarta mana irin jarumtar da marigayi matukin jirgin nan na rundunar, Baba Ari ya nuna lokacin da jirgin sa yayi tsari da na 'yan uwan sa a ragin Abuja cikin satin da ya gabata.

Kamar dai yadda muka samu, majiyar ta mu tace Marigayin ganin cewa jirgin nasa ya kwace kuma babu makawa sai a fado sai yayi anfani da basira irin wadda aka san shi da ita ya karkatar da jirgin daga cikin mutane ya zuwa wurin da ba kowa.

Allahu Akbar: Yadda Marigayi Baba Ari ya karkatar da jirgin sa daga cikin mutane kafin mutuwar sa
Allahu Akbar: Yadda Marigayi Baba Ari ya karkatar da jirgin sa daga cikin mutane kafin mutuwar sa
Asali: Twitter

KU KARANTA: An gano dakin taron 'yan Boko Haram

Legit.ng ta samu cewa wannan dai ba karamar dubara bace yayi inda hakan ya sa babu farar hula ko daya da hatsarin ya rutsa da shi sai dai su dake a ciki kawai.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa shugaban kasar Najeriya ma, Muhammadu Buhari yayi jimamin rasuwar sa tare da yin addu'a samun rahama ga mamacin.

A wani labarin kuma dai Dakarun sojojin saman Najeriya dake a rundunar nan dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da samun nasarar gano wani babban dakin taron 'yan ta'addan a kauyen Jabullam a can jihar ta Maiduguri tare kuma da yin raga-raga da shi.

Kwamandojin rundunar dake kula da harkokin yada labaran su ne dai, Air Commodore Ibikunle Daramola ya sanarwa da manema labarai hakan a garin Abuja lokacin da yake zantawa da su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel