An nuna fin karfi da ikon Jami’an tsaro a zaben Osun – inji UK, US, da EU

An nuna fin karfi da ikon Jami’an tsaro a zaben Osun – inji UK, US, da EU

- Jam'iyyar APC ta doke PDP ta lashe zaben Gwamna a Jihar Osun

- Kasashen sun fara nuna shakku game da adalcin Jami’an tsaro

- Ana zargin Jam'iyyar APC tayi amfani da karfin iko na Gwamnati

An nuna fin karfi da ikon Jami’an tsaro a zaben Osun – inji UK, US, da EU
An fara sa alamar tambaya bayan abin da ya faru a zaben Osun
Asali: Original

Mun ji labari cewa manyan Kungiyoyin kasashen waje irin su Amurka da Ingila sun fara nuna dar-dar bayan Jam’iyyar APC ta lashe zaben Gwamna a Jihar Osun inda ake tunani an yi amfani da karfin iko da kuma Jami’an tsaro a zaben.

Wani babban Jami’in Kasar Amurka John Bray wanda yana cikin wadanda aka yi zaben Jihar Osun a gaban su ya nuna cewa akwai matsala a zaben da aka gudanar na karashe inda ya tabbatar da cewa an nuna ikon Gwamnati.

KU KARANTA: Shugaba Buhari Mai gida na ne a Duniya inji Gwamnan Kudu

Jakaduna Amurka da na Kungyar EU ta kasashen Turai da Wakilan da Kasar Ingila ta aiko Najeriya sun tabbatar da cewa an yi amfani da sayen kuri’u da kuma razana masu kada kuri’u tare da ma hana wasu yin zaben a Osun.

Bray ya bayyana cewa ‘Yan daba sun yi amfani a wajen zaben sabon Gwamnan Jihar Osun da aka yi bayan da hotuna su ka nuna kuru-kuru yadda aka hana ‘Yan ganin kwa-kwaf da ‘Yan jarida da wasu masu kada kuri’u zuwa wajen zabe.

A wani jawabi da Jakadun kasashen wajen su ka fitar a Garin Abuja, sun ce zaben da APC ta lashe daga baya cike ya ke da rigima da hana wasu fita wajen zaben da sauran ba dai-dai ba iri-iri. Gboyega Oyetola na APC ne dai yayi nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel