Karin bayani: An sake gano wasu kayayakin Idris Alkali da ya bace a karkashin wani kududufi a Jos

Karin bayani: An sake gano wasu kayayakin Idris Alkali da ya bace a karkashin wani kududufi a Jos

- Hukumar Sojin Najeriya ta sake gano wasu kayayakin Sojan ta da bace a jihar Plateau, Janar Idris Alkali

- An gano motarsa ne a wata kududufi mai zurfi a garin Jos bayan an kwashe kwanaki ana nemansa

Hukumar Sojin Najeriya ta sake gano wadansu kayayakin Manjo Janar Idris Alkali bayan an gano motarsa a wani kududfi mai zurfi a Jos, babban birnin Jihar Plateau.

A wata sako da wani Idris Ahmed Ahmed ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ruwaito cewar an gano tufafi da takalman Manjo Janar mai murabus din a ranar Asabar 29 ga watan Satumba.

Duk da cewa har yanzu ba'a gano gawarsa ba, ana kyautata zaton an kashe shi kafin aka jefa kayayakinsa da motarsa a cikin kududufin.

Kaico: An sake gano wasu kayayaki mallakar babban sojan da aka kashe a Jos
Kaico: An sake gano wasu kayayaki mallakar babban sojan da aka kashe a Jos
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

Kaico: An sake gano wasu kayayaki mallakar babban sojan da aka kashe a Jos
Kaico: An sake gano wasu kayayaki mallakar babban sojan da aka kashe a Jos
Asali: Facebook

Ga abinda ya rubuta: "Zamu cigaba da kawo muku karin bayani kan kisar gillar da aka yiwa Manja Janar Idris Alkali. Bayan an gano motarsa a wata kududufi a Jos, an kuma gano wasu kayayakinsa daga cikin motar. Har yanzu dai ba'a gano gawarsa ba. Za mu cigaba da kawo muku karin bayani. Muna fatar Allah ya jikansa da Rahama. Amin."

Kaico: An sake gano wasu kayayaki mallakar babban sojan da aka kashe a Jos
Kaico: An sake gano wasu kayayaki mallakar babban sojan da aka kashe a Jos
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito cewa ana gab da a dakatar da neman da ake yiwa Idris Alkali ne kuma kwatsam sai aka ruwaito cewar an gano motarsa a wani kududufi a jihar Plateau.

An sanar da bacewar Alkali ne a ranar 3 ga watan Satumban wannan shekarar bayan ya baro Abuja a hanyarsa ta zuwa Bauchi. Alkali tsohon ma'aikaci ne a hedkwatan Sojin Najeriya da ke Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel