Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

Shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki ne ke kan gaba a wata zaben jin ra'ayi da ke gudana a Twitter da aka shirya tsakanin masu neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP guda hudu kamar yadda muka samu daga Daily Trust.

An shirya zaben jin ra'ayin ne a shafin gwamnatin jihar Rivers @PDP_RIVERS inda aka bukaci 'yan Najeriya su kada kuri'unsu domin zaban dan takarar shugabancin kasa na PDP da suke son ya lashe zaben fidda gwani domin ya yi takara a PDP a 2019.

Zaben jin ra'ayin ya ce, tunda jam'iyyar PDP wato @OfficialPDPNig ta tabbatar cewa za ta gudanar da zaben fidda gwani a ranar Asabar 6 ga watan Ocktoban 2018. Wane dan takarar jam'iyyar ku ke ganin zai iya kayar da shugaba Buhari na APC a zaben 2019.

DUBA WANNAN: 2019: Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo

Sai dai zaben ya lissafa 'yan takara guda hudu ne kawai wanda suka hada da, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

A lokacin wallafa wannan rahoton, mutane 5,596 ne suka kada kuri'unsu kuma Bukola Saraki ke kan gaba da 41%, mai biye masa kuma shine Atiku Abubakar da 30%, sai Rabiu Kwankwaso mai 21% kana Aminu Tambuwal na da 8%.

Sai dai har yanzu ana cigaba da kada kuri'u kuma za'a kwashe kwanaki hudu nan gaba kafin an kammala zaben jin ra'ayin kuma a sanar da wanda ya yi nasara baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel