Abun bakin ciki: An gano motar Janar din soja da ya bace a karkashin wani tafki mai zurfi a Jos, hotuna

Abun bakin ciki: An gano motar Janar din soja da ya bace a karkashin wani tafki mai zurfi a Jos, hotuna

Hukumar sojin Najeriya ta gano motar Janar (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa.

Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja. Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu.

Babu tabbacin ko gawar Alkali na cikin motar. Sai dai Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban rundunar soji dake farautar neman inda Janar din yake, ya bayyana cewar zasu kwashe ruwan domin tabbatar da gawar Alkali na ciki ko akasin haka.

Abun bakin ciki: An gano motar Janar din soja da ya bace a karkashin wani tafki mai zurfi a Jos, hotuna
motar Janar Alkali
Asali: Twitter

Tun a ranar 20 ga wata ne, Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.

DUBA WANNAN: Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna

A cewar Mohammed, bayanai na bayan-bayan nan da suka samu sun tabbatar masu da ganin motar janar Alkali daf da wani tafki a yankin.

Abun bakin ciki: An gano motar Janar din soja da ya bace a karkashin wani tafki mai zurfi a Jos, hotuna
Motar Janar Idris Alkali
Asali: Twitter

Mun zo nan ne bayan samun sahihan bayanai. Mun samu kusan tsawon sati guda muna nan, neman jami’in soja, Manjo Janar M. Alkali (mai ritaya), da har yanzu ba a san inda yake ba,” a cewar Mohammed.

Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.

Abun bakin ciki: An gano motar Janar din soja da ya bace a karkashin wani tafki mai zurfi a Jos, hotuna
Ruwan da aka gano motar Janar Idris Alkali
Asali: Twitter

A cewar Mohammed, bayanai na bayan-bayan nan da suka samu sun tabbatar masu da ganin motar janar Alkali daf da wani tafki a yankin. “Mun zo nan ne bayan samun sahihan bayanai. Mun samu kusan tsawon sati guda muna nan, neman jami’in soja, Manjo Janar M. Alkali (mai ritaya), da har yanzu ba a san inda yake ba,” a cewar Mohammed.

Mun zo har inda tafkin rowan yake domin ganin ko zamu samu wani abu da zai kai mu ga gano inda Janar Alkali yake. Wasu bayanai da muka samu sun bayyana cewar an tura wasu motoci cikin tafkin rowan. Rowan yana da zurfi sosai saboda wuri ne da ake hakar ma’adanai. Yanzu haka mun yanke shawarar yashe ruwan tafkin domin samun dammar ganin abinda ke can kasa,” kamar yadda Mohammed ya fada.

Janar Alkali ya bata ne ranar 3 ga watan Satumba bayan ya bar Abuja zuwa Bauchi cikin wata bakar mota kirar Toyoto Corolla. Duk kokarin samun shi ya ci tura saboda wayar sa a kashe take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel