A shirye nake na yi bautar kasa - Ministan Buhari

A shirye nake na yi bautar kasa - Ministan Buhari

- MInistan Sadarwa, Mr Adebayo Shittu ya ce a shirye ya ke ya yi hidimar kasa (NYSC) idan hakan ta kama

- Mr Shittu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a kafar yada labarai kwanaki biyu kafin APC ta soke takararsa

- Shittu ya ce an zabe shi a matsayin dan majalisar jiha ne shi yasa baiyi hidimar kasar ba amma NYSC bata gamsu da hakan ba

Ministan sadarwa na Najeriya kuma daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jihar Oyo, Adebayo Shittu ya ce a shirye ya ke da ya koma domin ya yi hidimar kasa ta shekara daya da dokar Najeriya ta wajabtawa duk wani mai digiri.

Mr Shittu ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da wani sananen dan jarida, Edmund Obilo a wata shirin da ake tattauna lamuran yau da kullum.

A shirye na ke inyi hidimar kasa - Ministan Buhari
A shirye na ke inyi hidimar kasa - Ministan Buhari
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Abin boye ya fito: Sirrukan sabon gwamnan Osun, Oyetola, da baku sani ba

Duk da cewa jam'iyyar APC ta ki tantance Shittu saboda rashin takardan kammala NYSC da bashi da ita a ranar Alhamis, wannan hirar anyi ta ne ranar Talata amma sai Asabar aka yada ta.

Ministan ya ce bai yi hidimar kasa bane saboda an zabe shi a matsayin dan majalisar jiha a lokacin da ya kammala jami'a sai dai hukumar NYSC ba ta gamsu da wannan dalilin da ya bayar ba.

Sai dai a hirar da a kayi da Shittu kwanaki biyu kafin jam'iyyar APC ta soke takararsa, Ministan ya ce a shirye ya ke ya yi hidimar kasar idan hakan ta kama.

Baya ga Shittu, jam'iyyar ta APC kuma ta soke takarar Ministan Harkokin mata, Aisha Alhassan saboda jam'iyyar ba ta gamsu da da'ar ta domin a lokuta da yawa ta sha fadin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ne mai gidanta duk da yana adawa da APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel