Boko Haram ta kashe wani Kwamandan ta da ya yi yunkurin mika wuya

Boko Haram ta kashe wani Kwamandan ta da ya yi yunkurin mika wuya

Mun samu cewa wani babban kwamanda na kungiyar ta'adda ta Boko Haram, ya yi gamo da ajali a hannun mabiyansa yayin da suka bankado wani sirrinsa na shirye-shirye da yunkurin mika wuya tare da ajiye makamansa na Yaki.

Daga wata majiya mai karfin gaske kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, mabiyan sun fusata a yayin da suka bankado sirrin kwamandansu na yunkurin mika wuya da kuma tserewa da kimanin mutane 300 da suka yi garkuwa da su cikin sansanin su.

Majiyar ta bayar da sunan wannan Kwamanda, Ali Garga, wani Bafulatanin Mutum dan asalin jihar Taraba da aka tursasa shiga wannan kungiya karkashin reshen ta na Mamman Nur shekaru uku da suka gabata bayan su kwace shanun sa na kiwo.

Ta ci gaba da cewa Garga ya zamto wata kadara mai girman gaske ga kungiyar, a sakamakon masaniya ta ilimin dajikan dake Arewa maso Gabashin kasar nan da ya mallaka a matsayinsa na Makiyayi.

Boko Haram ta kashe wani Kwamandan ta da ya yi yunkurin mika wuya
Boko Haram ta kashe wani Kwamandan ta da ya yi yunkurin mika wuya
Asali: Facebook

A sakamakon wannan ilimi na Dajikan Arewa maso Gabas da Gaga ya mallaka, kungiyar ta sanya shi cikin ta tare da koya masa yaki da kuma daukaka matsayin sa zuwa Kwamanda a karkashin reshen kungiyar Mamman Nur.

Sai da Garga ba ya da sha'awar ci gaba da wannan ta'addanci musamman garkuwa da Mutane, inda ya daura damara da yunkurin ajiye makamansa na yaki da komawa cikin ahalinsa inda zai ci gaba da sana'arsa ta kiwon shanu.

KARANTA KUMA: Wani 'Dan Kasar Ghana ya kashe Uwargidan sa a jihar Oyo

Majiyar ta kara da cewa, tuni Garga ya fara kulla shirye-shiryen sa tare da ganawa da wasu mutane a kasashen ketare da za su agaza wajen ceton sa da sauran wadanda ya nufaci tserewa tare da su kafin sauran 'yan uwansa su gano shirinsa.

Sai dai jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin hausawa kan ce kaddara ta riga fata Garga ya afka cikin abinda ya sha fargaba a kansa da a halin yanzu rayuwarsa a bisa doron kasa ta zamto tarihi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel