PDP tayi sabon shugaban jam'iyya a Legas

PDP tayi sabon shugaban jam'iyya a Legas

- Jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Legas ta nada sabon Ciyaman

- An nada Adegbola Dominic ne bayan tsohon Ciyaman din jam'iyyar, Moshood Salvador ya sauya sheka zuwa APC

- Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta kalubalanci sabon Ciyaman din ya hada kan 'ya'yan jam'iyyar

A yau, Asabar ne jam'iyyar PDP reshen jihar Legas ta sanar da cewa jam'iyyar ta zabi Adegbola Dominic domin maye gurbin tsohon Ciyaman din jam'iyyar, Moshood Salvador wanda ya sauya sheka zuwa PDP.

PDP tayi sabon shugaban jam'iyya a Legas
PDP tayi sabon shugaban jam'iyya a Legas
Asali: Twitter

Sanarawan da fito ne daga bakin, Mataimakin Ciyaman na kasa (Yankin Kudu maso Yamma), Mr Eddy Olafeso, inda ya ce gwamnatin gudanarwa na jam'iyyar ta yanke shawarar zabar Dominic a matsayin sabon shugaba.

DUBA WANNAN: Zaben fitar da gwani: Buhari ya samu kuri'u 388,653 a jihar Rivers

Mr Olafeso ya yi kira ga sauran jami'an jam'iyyar su hada karfi da karfe domin ganin cewa jam'iyyar tayi nasara a babban zaben 2019 mai zuwa.

Ya kuma ce jam'iyyar ta sanar da Sufeta Janar na 'yan sanda da Hukumar Zabe INEC da Direkta Janar na DSS cewa daga yanzu Mr Dominic ne zai rika juya lamuran jam'iyyar a jihar Legas a matsayinsa na sabon shugaba.

Daga karshe ya yi kira ga sabon Ciyaman din ya dauki matakan kawo hadin kai tsakanin ''ya'yan jam'iyyar musamman a yanzu da zabe ke karatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel