Babbar magana: An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya

Babbar magana: An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya

- An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya

- Wani tsohon soja ne ya kama shi

- Barawon shekarar sa 23 kacal a duniya

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Ogun dake a yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin kasurgumin barawo ne da kan sanya kayan sojoji tare da kwacewa jama'a kudaden su a Karamar hukumar Obafemi-Owode.

Babbar magana: An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya
Babbar magana: An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Saraki da Atiku sun bayyana ra'ayin su game zaben fitar da gwani da za'ayi a Fatakwal

Barawon dai wanda aka ce shekarun sa kwata-kwata 23 an kama shi ne wajen karfe 8 na dare jim kadan bayan da ya kwatar wa wani tsohon soja mai suna Adeyemo Adegboyega Naira 86,000 a tsakiyar watan nan da muke ciki.

Legit.ng ta samu cewa tsohon sojan ne da hadin gwiwar jami'an 'yan sandan suka bibiyi sawun barawon har kuma suka kama shi inda dubun sa ta cika.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi babban burin sa idan har Allah ya sa ya lashe zaben shugaban kasar da za'a gudanar a shekara mai zuwa ta 2019 shine na ya tabbatar da ya bar wani babban abun azu a gani a sha'anin mulkin kasar nan.

Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da 'yan Najeriya mazauna kasashen Amurka da kuma Kanada a yayin ziyarar da yanzu haka ya ke kan yi a kasar ta Amurka, birnin New York.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel