Babban buri na idan na lashe zaben 2019 - Shugaba Buhari

Babban buri na idan na lashe zaben 2019 - Shugaba Buhari

- Buhari ya fadi babban buri sa idan na lashe zaben 2019

- Yace yan burin maida Najeriya abun alfahari a duniya

- Ya fadi hakan ne a garin New York, kasar Amurka

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi babban burin sa idan har Allah ya sa ya lashe zaben shugaban kasar da za'a gudanar a shekara mai zuwa ta 2019 shine na ya tabbatar da ya bar wani babban abun azu a gani a sha'anin mulkin kasar nan.

Babban buri na idan na lashe zaben 2019 - Shugaba Buhari
Babban buri na idan na lashe zaben 2019 - Shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun gano dumbin kudaden jabu a wani Kango a Maiduguri

Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da 'yan Najeriya mazauna kasashen Amurka da kuma Kanada a yayin ziyarar da yanzu haka ya ke kan yi a kasar ta Amurka, birnin New York.

Legit.ng ta samu cewa haka ma Shugaban kasar ya kuma nuna rashin jin dadin sa game da yadda yace wadanda ke kiran kan su manya a Najeriya suka yi shiru shekaru 16 lokacin da jam'iyyar PDP ke mulkin kasa duk kuwa da yadda suka lalata kasar.

Ya kara da cewa hakan haka zalika abun takaici ne yadda kuma yanzu wasun su ke ta kumfan baki suna cewa wai baya da sauri bayan duka-duka shekaru 3 kadai yayi yana mulki.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa labaran da ake yadawa na cewa bai ji dadin kai zaben fitar da gwanin su ba a garin Fatakwal ba gaskiya bane.

Atiku wanda yace shi garin Fatakwal kusan gida ne a gare shi ya bayyana cewa baya ma bukatar masauki ko wani tsaro na musamman domin kuwa a yi wani bangare na rayuwar sa a garin a shekarun baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng