PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark

PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark

A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon shugaban majalisar dattawa kuma daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Sanata David Mark, ya bayyana yadda jam'iyyar za ta kasance bayan ta gudanar da zaben fidda gwani.

Sanata David Mark ya kyautata zatonsa da cewa, jam'iyyar ta PDP ba za ta tarwatse ba koda kuwa bayan an kammala zabenta na fidda gwanin da zai rike mata tutar takarar kujerar shugaban kasa a 2019.

Yake cewa, akwai barazanar jin kunya da kuma shan takaici ga duk wanda ba su tashi sun farga ba kuma suke hasashen za a fuskanci mummunan rikici da rashin jituwa bayan an gudanar da zaben fidda gwanin takara na jam'iyyar.

PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark
PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark
Asali: Depositphotos

Tsohon shugaban majalisar ya yi bugun kirji da cewa, sabanin rashin kyawun zato da hasashe da wasu mutane ke yi kan yadda jam'iyyar za ta kasance bayan zabenta na fidda gwani, jam'iyyar za ta kara karfafa ta fuskar hadin kai da mai karfin gaske.

KARANTA KUMA: Zaben Jihar Osun: Al'ummar Gabashin Najeriya za su kauracewa Zaben shugaban kasa a 2019

Sanata David Mark ya na kuma da yakini da cewa, akwai goyon bayan mai tsananin amincin da jam'iyyar za ta bai wa duk wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin takarar kujerar shuagaban kasa kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon shugaban majalisar ya yi wannan furuci yayin gabatar da jawabansa a babban ofishin jam'iyyar sa dake birnin Minna na jihar Neja, inda ya bayar da tabbacin sa kan cewa za a gudanar da tsaftataccen zabe da ya tsarkaka daga duk wani magudi ko rashin adalci yayin fidda gwani na jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel