Zaben Jihar Osun: Al'ummar Gabashin Najeriya za su kauracewa Zaben shugaban kasa a 2019

Zaben Jihar Osun: Al'ummar Gabashin Najeriya za su kauracewa Zaben shugaban kasa a 2019

Wata kungiya ta al'ummar yankin Gabashin Najeriya ta ECA (Eastern Consultative Assembly), ta bayyana fushinta da kuma takaici tare da yin tir da wus kan zaben gwamnan jihar Osun da ta bayyana shi a matsayin mafi kololuwar zalunci.

A sanadiyar haka kungiyar ta yanke shawarar kauracewa zaben shugaban kasa a 2019 a yayin da jam'iyyar APC ta bayyana karara kuri'un al'umma ba su da wani tasiri kan sakamakon zabe kamar yadda kungiyar ta bayyana.

Kungiyar ta bayyana hakan ne da sanadin mataimakin shugaban ta da kuma sakataren ta, Evangelist Elliot da Ugochukwu-Uko, bayan ta gudanar da wani taro cikin jihar Enugu a ranar Alhamis din da ta gabata.

Zaben Jihar Osun: Al'ummar Gabashin Najeriya za su kauracewa Zaben shugaban kasa a 2019
Zaben Jihar Osun: Al'ummar Gabashin Najeriya za su kauracewa Zaben shugaban kasa a 2019
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar ta yanke wannan shawara ta kauracewa zaben shugaban kasa a 2019 da cewar ba bu wata hanya da za a gudanar da duk wani zabe da zai tsarkaka da magudi da rashin gaskiya a karkashin jagorancin jam'iyyar APC.

Kungiyar ta bayyana zaben gwamnan jihar tamkar wani fashi da makami da rana tsaka da hakan ya kawar da duk wani shakku dake zukatan al'ummar kasar nan da ba bu wani zabe da zai gudana a kasar nan face mai cike da mafi kololuwar magudi na zalunci.

KARANTA KUMA: Jadawalin Zaben fidda Gwanayen takara na jam'iyyar APC

Kazalika kungiyar ta bayyana yadda hukumomin tsaro na kasar nan suka mamaye jihar ta Osun a yayin zaben gwamnan a matsayin wata kitimurmura ta jam'iyyar APC bisa jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin cin karen su ba bu babbaka.

Bugu da kari kungiyar ta nemi afuwar kungiyar masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara ta IPOB da tun fi azal ta fahimci duk wani tuggu da gwamnatin jam'iyyar APC ke kullawa a kasar nan na kudirta aiwatar da magudi a kowane zabe da za a gudanar cikin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel