Babban magana: 'Yan sanda sun damke dan fashi sanye da khakin sojoji

Babban magana: 'Yan sanda sun damke dan fashi sanye da khakin sojoji

Jami'an 'yan sanda Najeriya reshen jihar Ogun sun damke wani Adeoye Ayomide sanye da kayan sojoji yana taimakawa wasu abokansa wajen yiwa mutane fashi da makami.

Kakakin 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya shaidawa Premium Times a yau Juma'a cewa an damke Ayomide ne a Ofada Road da ke Mawe a karamar hukumar Obafemi-Owode da ke jihar Ogun.

An kama Ayomide ne misalin karfe 8 na daren tare da abokansa bayan sun yiwa wani tsohon soja mai murabus, Adeyemo Adegboyega fashin N86,000 a ranar 13 ga watan Satumban 2018 ta hanyar yi masa barazana da kwalba.

Babban magana: 'Yan sanda sun damke dan fashi sanye da khakin sojoji
Babban magana: 'Yan sanda sun damke dan fashi sanye da khakin sojoji
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Mai rabo ka dauka: APC ta amince da takarar mutane 3 da ke burin kayar da gwamna Abubakar

Shi kuma tsohon sojan ya garzaya zuwa ofishin yan sanda da ke Mowe inda ya shigar da kara kana dan sanda, Francis Ebuhoma ya jagoranci wasu 'yan sanda su ka bi sahun barayin.

Asirinsu ya tonu ne a ranar Talata bayan 'yan sandan sun sami labarin cewa an hangi 'yan fashin a Mowe. Yan sandan ba suyi wata-wata ba wajen garzayawa unguwar inda suka damke daya daga cikin yan fashin sanye da kayan sojoji.

Kakakin 'yan sandan ya ce hukumar ta nemi izinin gudanat da bincike a gidan wanda ake zargi inda aka gano karin kayayakin sojoji na bogi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu ya bayar da umurnin a tura binciken zuwa sashin 'yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami wanda akafi sani da FSARS domin cigaba da binciken.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel