Hukumar NPS ta sallami jami’ai 3 kan safarar wasu haramtattun kayayyaki da ka iya barazana ga tsaro a gidan yari

Hukumar NPS ta sallami jami’ai 3 kan safarar wasu haramtattun kayayyaki da ka iya barazana ga tsaro a gidan yari

Kwanturola janar na hukumar gidan yari, Ja’afaru Ahmed ya amince da sallaman kananan jami’an hukumar guda uku kan safarar wasu haramtattun kayayyaki da ka iya kasancewa barazana ga tsaron gidan yarin.

Wadanda aka sallama sun hada da IP Samaila Inusa, PA 11 Jonathan Ibrahim da kuma PA 11 Adamu Jethro.

Hakan ya biyo bayan shawarar da kwamitin da’a ta bayar bayan ta kama su da laifin shigar da haramtattun kayayyaki kamar su tabar wiwi da sauran kayan maye ga ýan gidan yari.

Hukumar NPS ta sallami jami’ai 3 kan safarar wasu haramtattun kayayyaki da ka iya barazana ga tsaro a gidan yari
Hukumar NPS ta sallami jami’ai 3 kan safarar wasu haramtattun kayayyaki da ka iya barazana ga tsaro a gidan yari
Asali: Depositphotos

A lura cewa baya ga rashin da’a da barazana ga lafiyar yan gidan yari da abun zai yi, mallakar kayan maye da tabar wiwi ya sa yin sanadiyar da wasu mutane ke tserewa daga gidan yari a baya.

KU KARANTA KUMA: 'Yan kwagila masu shgo da mai sunce gwamnatin Tarayya tayi hobbasa ta biya su bashin N650b

Barazana ga tsaro na iya kai ga sarar rayuka da dukiyoyin jami’ai da mutanen dabasu jib a basu gani ba.

Shugaban hukumar ya sha alwashin tabbatar da hukunta duk jami’in da aka kama da laifin da ka iya zama barazana ga tsaro kamar yadda doka ta tanadar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel