Zaben fitar da dan takarar APC: Har yanzu ba'a fara zabe a jihar Nasarawa ba

Zaben fitar da dan takarar APC: Har yanzu ba'a fara zabe a jihar Nasarawa ba

- An samu jinkirin fara gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa ta APC a jihar Nasarawa

- Sakataren shirye-shirye na jihar, Hassan Wali ya ce za'a fara zaben ne misalin 11.20 na safiyar yau amma har zuwa 11 mutane basu hallara ba

- Wannan ya sha ban-ban da wasu jihohin da tuni mutane suka hallara wuraren kada kuri'un domin nuna goyon bayansu ga shugaba Buhari

A yayin da tuni wasu johihi sun fara kada kuri'unsu a zaben fiddar da gwani na shugabancin kasa a jam'iyyar APC, rahotonin da muka samu daga Daily Trust ya ce har yanzu ba a fara zaben ba a birnin Lafiya da wasu manyan birane a jihar Nasarawa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa jami'inta da ke Lafia ya zagaya cikin garin tun daga karfe 8 na safe har zuwa 12 na rana amma bai taras da inda ake jefa kuri'ar na zaben fitar da gwanin ba.

An samu jinkirin fara zaben fidda gwani a wata jihar Arewa
An samu jinkirin fara zaben fidda gwani a wata jihar Arewa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya

An ruwaito cewar babu alamun masu kada kuri'un a mazabun Chiroma, Gayam, Shabu da Agyaragun Tofa inda aka gano yara sun buga kwallon kafa a wuraren da ya kamata ake gudanar da zabukkan na fitar da gwani.

Da aka tuntubi Hassan Wali, sakataren shirye-shirye na jihar ya ce za'a fara gudanar da zaben fitar da gwanin ne misalin karfe 11.20 na safiyar yau, ya kuma ce za'a gudanar da zabukkan ne a hedkwatan sakatariyar jam'iyyar da ke mazabu ba Sakatariyar Jihar ba.

Legit.ng ta ruwaito cewa tuni an fara gudanar da zabukkan fitar da gwanin a wasu jihohi inda alamu ke nuna shugaba Buhari yana samun nasara sosai duba da yadda mutane suka hallara domin kada kuri'unsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel