Yan ta'adda sun kai sabon hari a sakatariyar jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa

Yan ta'adda sun kai sabon hari a sakatariyar jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa

- Yan ta'adda sun kai hari a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke a jihar Bayelsa tare da kuma bude wuta akan jami'an tsaro dake yankin

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan da suka kunshi gungun mutane 5, karkashin uban dabar Aboye, sun fito ne daga jihar Rivers

- Shuwagabannin yankin Sun yi zargin cewa yan ta'addan sun kai harin ne bisa umurnin jam'iyyar hamayya ta APC

A ranar Alhamis ne wasu da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne suka tayar da hankulan al'ummar Brass Island da ke jihar Bayelsa, inda suka kai hari a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke a yankin tare da kuma bude wuta akan jami'an tsaro dake yankin.

Wannan yazo ne gabanin kai wani mummunan hari da yan ta'adda suka yi ga dan takarar majalisar wakilai ta tarayya karkashin jam'iyyar APC a jihar Ondo, Mr Olatayo Aribo, inda suka cinnawa daya daga cikin motocin yakin zabensa wuta.

Dangane da ta'addancin Bayelsa kuwa, an samu katsewar harkokin kasuwanci da sauran hada-hadar yau da kullum bayan da magoya bayan jam'iyyar PDP da ke a yankin da lamarin ya shafa suka gudu daga gidajensu a safiyar Alhamis don tsira da rayukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan da suka kunshi gungun mutane 5, karkashin uban dabar Aboye, sun fito ne daga jihar Rivers, inda suka fatattaki mazauna yankin a safiyar ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN: Ma'aikata sun maka kamfanin Unilever a kotu

Yan ta'adda sun kai sabon hari a sakatariyar jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa
Yan ta'adda sun kai sabon hari a sakatariyar jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa
Asali: Facebook

An bayyana cewa sun yi harbe harben kan mai uwa da wabi don tosrarta da jama'a kafin daga bisani suka kai wa sakatariyar harin.

Da su ke jawabi ga manema labaria a garin Yenagoa a ranar Alhamis, shugaban riko na karamar hukumar Brass, Victor Isaiah; mataimakin kakakin majalisar dokoki ta juhar, Abraham Ingobere; da kuma sanata mai wakiltar Bayelsa ta Kudu a majalisar dattijai, Ben Murray-Bruce, sun yi Allah wadai da wannan harin.

Sun yi zargin cewa yan ta'addan sun kai wannan mummunan harin ne bisa umurnin jam'iyyar hamayya ta APC da ke a yankin.

Sun yi kira ga Sifeta Janar na rundunar yan sanda da sauran jami'an tsaro da ke a jihar da su tashi tsaye haikan don kare rayuka da dukiyar al'ummar yankin daga hare haren 'yan bangar siyasa a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel